A kasa da shekara biyu a mastayinsa na shugaban Hukumar Tashoshin Ruwan Nijeriya NPA Mohammed Bello Koko ya samar da gaggarumin ci gaban da aka dade ba a samu irinsa ba.
Tashoshin ruwa na Nijeriya na ta dawo da kayan da aka yi hasararsu a baya ga kasashen da ake da makwabtaka da su sakamakon bunkasar ingantacciyar hanyar samar da kayayyaki, ingantacciyar yadda ake gudanar da zirga-zirgar ababen hawa, da saukin zirga-zirgar kayayyaki a tashoshin jiragen ruwa.
Kafin yanzu, an san tashar jiragen ruwa ta Nijeriya a matsayin daya daga cikin mafi tsada da rashin inganci a yankin Afirka ta Yamma da ta Tsakiya. Wannan ya sanya tashar ta kasance ba ta jan hankalin masu shigo da kaya ba, inda suka gwammace da su karkatar da kayayyakin da za su je Nijeriya zuwa tashoshin jiragen ruwa masu inganci a yankin.
Hakan ya faru ne saboda matsalolin da ke tattare da lalacewar kayayyakin jigila ta tashar jiragen ruwan, daukar dogon lokaci wajen dakon kaya, rashin ingancin jujjuyawar jirgin ruwan, daukar dogon lokaci wajen aikin sharer fage, da cunkoso da ke haifar da cunkoson ababen hawa a cikin tashar jiragen ruwan.
Wadannan kalubalen sun haifar da masu shigo da kaya na karkatar da kayayyakin zuwa kasashen makwabta, wanda hakan ya haifar da illa ga bunkasar hanyoyin kudaden shiga na kasa da kuma yadda ake sarrafa kayayyakin.
Sai dai al’amura sun fara daidaita, biyo bayan yunkurin da shugabancin hukumar NPA na yanzu ke yi na aiwatar da gyare-gyare tare da dawo da ka’ida a tashoshin jiragen ruwa.
An nada Bello-Koko a matsayin Manajan Darakta na hukumar a ranar 6 ga Mayu, 2021 a matsayin mukaddashi, sai dai an tabbatar da shi a ranar 21 ga Fabarairu, 2022. Tun daga wannan lokacin, tawagar Bello-Koko ta dukufa wajen sauya yadda lamura ke gudana.
A yanzu haka, tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya sun zama abin da aka fi so a yammacin Afirka, musamman ga kasashen da ba su da tudu kamar Jamhuriyar Nijar, wadanda ke nuna sha’awar jigilar kayansu daga Nijeriya.
Kammala tashar jiragen ruwa mai zurfi ta Lekki, daukar nauyin gyaran manyan titunan tashar jiragen ruwa da suka lalace, tare da kawo karshen cunkoso a tashoshin jiragen ruwa da kuma a hanyar tasoshin jiragen ruwan ta hanyar tabbatar amfani da na’urar kiran waya na daga cikin hanyoyin da hukumar ta ke samun nasarar tsaftace tashar jiragen ruwan.
Fiye da wannan, NPA a karkashin wannan shugabanci ta habbaka ayyuka a fannoni kamar:
Tara Kudade Zuwa Asusun Tarayya
Hukumar NPA karkashin Bello-Koko tana tallafawa tattalin arzikin kasa ta hanyar tara kudaden shiga da ba a taba ganin irinsa ba tare da turawa asusun hadakar kudaden shiga (CRF). Kudaden shiga na hukumar ya karu daga Naira biliyan 317 a shekarar 2020 zuwa Naira biliyan 361 a shekarar 2022, yayin da kudaden da ake aikawa da su ya karu daga Naira biliyan 80 a shekarar 2020 zuwa Naira biliyan 91 a shekarar 2022.
Binciken Businessday ya nuna cewa NPA a karkashin wannan jagorancin na yanzu ya nuna ta samar da sabbin sana’o’in da ba wai kawai sun samar wa ‘yan Nijeriya ayyukan yi ba, har ma sun kasance hanyoyin samun kudaden shiga.
Sun hada da samar da ayyukan jiragen ruwa, wanda baya ga rage matsi a titunan, ya kuma bunkasa har ya kai kasuwancin Naira biliyan 2, wanda hakan ya jawo jarin kai tsaye.
An yi bitar hauhawar hayan gidaje domin ya dace da halin da ake ciki na tattalin arziki da nufin inganta kudaden da hukumomi ke samu daga kula da kayyadaddun kadarorinta.
Har ila yau, ta ba da lasisin karin wuraren ajiya na manyan motoci domin kara karfin manyan motocin da ke aiki a tashoshin jiragen ruwa na Legas, da kuma bayar da lasisin guda 10 na Tashar fitarwa ta ‘Edport Processing Terminals (EPT)’ domin saukake fitar da kaya a tashar jiragen ruwa. Tashar ta samar da shagon tsayawa guda daya wanda ke ba da damar sarrafa inganci, tantance kaya daga dukkan hukumomin gwamnati, da kuma ba da izinin jigilar kayayyaki.
A yanzu, an sami gagarumin ci gaba ta fuskacin lokacin juyar da manyan motoci saboda nasarar aiwatar da tsarin kiran na zamani.
Domin tabbatar da bin tsarin kiran wayar, NPA ta tura babura 24 domin taimakawa wajen sa ido kan manyan motocin a mashigar Apapa/TCIPC/Ijora da kuma dorewar zirga-zirgar ababen hawa ba tare da cunkoso ba. Har ila yau, ta yi hadin gwiwa da jami’an ‘yan sanda domin katse shingayen binciken ababen hawa wadanda suke ba bisa ka’ida ba da ke kan hanyar tashar jiragen ruwa tare da kuma dakile cutar al’umma domin a samu nasarar tafiyar da ababen hawa cikin inganci.
Inganta Kayan Aikin Sintiri Da Kuma Tsaron Tashar Jiragen Ruwa
Hukumar NPA a karkashin Bello-Koko ta samar tare da girka ‘fairway buoys’ guda 86 a yankunan Warri da Calabar Pilotage domin ba da damar yin alamar tashoshi da taswirar hanya. Har ila yau, ta kuma samar da kananan jiragen ruwa, da suka hada da jiragen ruwa, ‘pilot cutters’, da jiragen sintiri, domin kawar da jinkirin da ke da nasaba da jigilar jiragen ruwa da tuki tare da bunkasa inganci. Har ila yau, ta sayo tare da tura kwale-kwale na jami’an tsaro zuwa dukkan gundumomin matukan jirgi domin magance hare-hare da ake kai wa jiragen ruwa a kan tashoshi da mashigin ruwa.
Habaka Kayayyakin Gudanarwa Da Kuma Ababen More Rayuwa
A cikin shekarar da ta gabata ne, jagorancin NPA ya kirkiro tashar siginar da za ta baiwa NPA damar ta kama motsin jiragen ruwa masu yawa. Har ila yau, an kammala binciken aikin wanke datti na barkewar hanyoyin ‘Escrabos’ domin kara karfin rike kwantena a tashar ruwan Ribers sakamakon sauya sararin da ba a yi amfani da shi ba a cikin tashar PTOL a tashar ruwan Ribers zuwa wurin da aka tattara.
Sauran sun hada da inganta ababen more rayuwa a tashar ‘B’, Berths 7 da kuma 8, da kuma tashar jiragen ruwa ta Onne ta hanyar hadin gwiwar gwamnati da kamfanuka masu zaman kansu (PPP) na gammayar kamfanin WACT Nigeria Limited wanda ya kai kimanin dala miliyan 110 a tsawon shekaru biyu. Wannan ya zuwa yanzu ya kai kashi 62 cikin dari na kammalawa.
Hukumar ta NPA ta kuma ba da izini ga gamayyar kamfanin Ringadars domin gina tankunan ‘bitumen metric’ mai daukar tan 6,000 a cikin tashar ruwa ta Ribers domin inganta karfin ajiyar ‘bitumen’ na kamfanin, wanda zai saukaka aiki tare da yin tasiri ga ci gaban ababen more rayuwa na Kudu maso Kudu. Ya zuwa yanzu dai an kammala aikin da kashi 58 cikin dari.
Jagorancin wannan hukumar a halin yanzu sun kasance a gaba wajen gwagwarmayar gyara abubuwan da suka lalace a tashar jiragen ruwa kuma sun kara samun amincewar gina katangar jinginar jiragen ruwa a mai lamba 15 a tashar jirgin ruwa ta Legas dake Apapa. Har ila yau, ta amince da kammala aikin hanyar zamani domin hadakar lamba ta 9, 10, da 11 a tashar jirgin ruwa ta Tarayya da ke tashar Onne.
Bello-Koko ya kuma samu amincewar sake gyara tasoshin kula da tashoshin jiragen ruwa na Legas da Tin-Can Island tare da samar da kuma sanya kariyar ruwa 180 domin inganta katangar kariya tare da kuma zama matakin riga-kafi domin dakile duk wani hatsari da ya taso daga jirgin ruwan kai tsaye zuwa katangar kariyar.
Hukumar ta NPA ta kammala ayyukan tuntubar juna domin kariya ga bakin ruwa da kuma gyara magudanar ruwa na Escrabos da kuma bincike da taswirar gundumar Warri Pilotage tun daga babbar titin Warri-Sapele har zuwa tashar Koko.
Tare da kaddamar da tashar ruwa mai zurfi ta Lekki cikin lokaci, NPA ta sami amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya domin fara aikin gina tashar jiragen ruwa na Badagry, tare da kuma bayar da tallafi domin kafa tashoshin Ondo da Benin.
Kulla Alaka Da Bankin Duniya Da IFC
NPA ta sa Bankin Duniya da Hukumar Kula da Kudade ta Duniya domin ta samar da wata hanyar kudade domin bunkasa ababen more rayuwa ta tashar jiragen ruwa.
Ingantattun Bayanai Da Kuma ICT
Daya daga cikin abubuwan da ke kawo cikas ga ci gaba a fannin lura da tasoshin ruwa shi ne samun sahihan bayanai domin tsarawa. Sai dai tun bayan hawan Bello-Koko, shugabancinsa ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) domin nadar bayanai a zamanance domin musanya domin hada kididdigar tashoshin jiragen ruwa da kundin ajiye bayanai na kasa.
Shugaban NPA ya kuma sami sahhalewar domin bunkasa shafin Intanet na hukumar da kuma shafin Intanet na zirga-zirgar jiragen ruwan domin zama mai saukin amfani kuma domin sarrafa bayanai ta atomatik.
Hukumar ta kulla alakar aiki tare da Hukumar Kula da Ruwa ta Duniya (IMO), kan habaka tsarin tasoshin hukumar domin sarrafa ayyukan tashar jiragen ruwa a zamance.
Wannan ya biyo bayan bayar da kwangilar sabis na tuntuba domin lura da zirga-zirgar jiragen ruwa (BTS), ma’auni na aminci na lura da tasoshin ruwa wanda ke da damar wayarwa domin bai wa NPA damar samun jagora tare da samar da bayanan aminci ga jiragen ruwa a cikin tashoshin a bisa tsarin doka na kare rayuwa a tasoshin ruwa (SOLAS).
Jindadin Ma’aikata
A tarihi yake cewa Bello-Koko shi ne Babban Manajan Daraktan Hukumar na farko da ya tabbatar da ya samo amincewar karin albashin ma’aikata wanda ya tsaya cak a tsawon shekaru 15. Ya kuma kara da tabbatar da biyan kudaden fansho da kudaden ritaya ga wadanda suka yi ritaya cikin gaggawa.
Har ila yau, ya kuma tabbatar da karin girma ga ma’aikatan da suka cancanta cikin gaggawa tare da amsa bukatun kungiyoyin ma’aikatan tasoshin ruwa. Shugabancin hukumar NPA na yanzu ta gyara Cibiyar Horarwa ta Dockyard a Apapa domin ma’aikata, membobin tashar jiragen ruwa, da kuma kungiyoyin kamfanoni masu sha’awa. Mataki ne na rage kashe kudi wanda aka yi da nufin kula da albarkatu.
Ayyukan Taimakon Al’umma (CSR)
Ta fuskar CSR, shugaban hukumar NPA ya samar da ingantattun kayan wasanni da cikakken kayan aiki ga dukkanin makarantun firamare da sakandare na karamar hukumar Surulere da kewaye da ke amfani da su, tare da gyarawa da samar da kayan aiki ga babban asibitin karamar hukumar Apapa da kuma Bonny.
Har ila yau, ya samu saya tare da rarraba injunan dinki da nika domin karfafa al’ummomin da ke da kusa da tashar jiragen ruwa a Ribers, Calabar, da Warri domin habaka karfin kasuwanci a tsakanin kananan ‘yan kasuwa. Har ila yau, ya ci gaba da yin hulda tare da al’ummomin da suka karbi bakuncin tasoshin jiragen ruwan ta hanyar masu kula da tashar jiragen ruwa.
Bincike ya nuna cewa sauya fasali na hukumar da Bello-Koko ya soma ya samar wa da NPA nasarar lashe kyauta a mataki na 5 na ‘Platinum Lebel’ daga ofishin sake fasalin ma’aikatan gwamnati (BPSR) sakamakon samar da yanayi na samar da ayyuka masu inganci a kowane fanni.