Mata masu shayarwa da kananan yara a Jihar Borno, sun fara bin gidan tururuwa suna neman abinci, sakamakon ta’azzarar rashin abinci da karuwar cutar tamowa.
Mazauna wasu yankuna a Jihar Borno da ma’aikatan kiwon lafiya, sun shiga damuwa game da karuwar yara masu tamowa a jihar.
- Girman Manzon Allah (SAW): Darasi Daga Suratul Fat’hi (I)
- Matsalar Tsaro Da Hadurran Kwalekwale Da Ambaliyar Ruwa Na Cin Rayuka A Arewa
Abin da suka ce na da nasaba da rashin wadataccen abinci mai gina jiki ga mata masu shayarwa.
Bugu da kari rahotanni sun nuna cewa kananan hukumomi bakwai ne a jihar Borno, matsalar ta fi shafa.
Kananan hukumomin sun hada da Marte da Kukawa da Abadam da Guzamala da Kaga da Mobar da kuma Gubio.
Yaran da ke a wadannan yankuna sun dogara ne da tallafin da suke samu daga kungiyoyin agaji.
Wata mata da ke aiki a kungiyoyin agaji, Fatima Muhammed Habib, ta manema labarai cewa, a da mutane ba su san ana fama da wannan matsala ba.
”Da muka je daya daga cikin wadannan yankuna mun tarar rabin yaran garin na fama da matsalar abinci mai gina jiki, haka suma matan da ke shayarwa, za ka gan su duk a wahale babu wani abinci mai maiko ko kyau da suke samu suna ci ga shi kuma suna shayarwa.”
Ta ce idan har uwa ba ta ci ta koshi ba ta yaya za ta samu ruwan nono bare har ta shayar da danta?
“Saboda tsananin yunwa haka za ka ga mata na tona gidan tururuwa don samu abinci, haka mata ke kungiya suna yawo don neman gidan tururuwar da za su samu abinci.”
“Babban abin tashin hankali shi ne daji matan ke zuwa don su samo gidan tururuwar, ga rashin tsaro a wuraren ga macizai da dai sauransu.” Ta ce suna kai musu taimako, amma taimakon ba lallai ya isa ba.
Yadda Lebura Ke Neman Abinci A Ramin Tururuwa A Bauchi
Idan ba a manta a Jihar Bauchi ma irin haka ta faru a watan Fabrairn 2024, inda leburori masu aikin karfi, suka koma tona gidan tururuwa domin neman abin da za su ci dangane da abin da suka kira na rashin ayyukan yi musamman tun daga lokacin da aka janye tallafin man fetur a Nijeriya.
Jaridar The Eagle-Eye Daily Post, ta ruwaito yadda ta taba cin karo da wani mutum mai aikin karfi mai suna Abubakar Salisu Na-giyade a Ibrahim Bako Bye-pass, inda ya hada zufa yana tona gidan tururuwa da nufin neman shinkafar da suka tara.
Leburan ya ce akwai ramin da ya samu kusan mudu biyu a ranar, yanzu kuma ya koma kan sabon rami wanda idan ya dace, zai iya hada mudu biyar idan aka gyara za a iya samun mudu biyu na shinkafar tuwo da kudinsu ya kai Naira 3,400 a wancan lokaci.
Ya ce a leburancin yini guda, ba ya wuce a biya mutum Naira 2,000 ko 3,000, shi ma aikin ba a cika samu a yanzu ba duba da yadda al’amura suka tsefe.
A cewarsa gyaran masai (shadda) ne, idan suka samu ake biyan ma’aikaci Naira 5,000 zuwa 10,000, wanda shi ka ya ce ba mutum daya ake bai wa kudin ba.
Leburan, ya ce yana da mata guda daya da yara takwas, ya kara da cewar dole ce ta sa ya fara aikin tona ramin tururuwa, tun da ya fahimci wani lokacin an fi samun abinci a wajen.
Kazalika, ya ce idan ya samo abinci a can sai dai kawai ya ji da na cefane ko kuma su bayar da shinkafar a ba su masara don su yi cefane kuma a haka suke rayuwa.
Ya ce yanzu haka, yana da ‘yan mata hudu wasu daga cikinsu sun kamala makarantun f6iramare da karamar Sakandare, amma rashin kudi ya sa suna zaune tare da su a gida sai Islamiyya da suke zuwa wanda malaman ko Naira 100 aka ba su suna hakuri.
A gefe guda leburan ya koka baya ga tsadar rayuwa, ya ce a gidan haya yake zaune ga kuma tsadar kudin sufuri, wanda hakan ya sa yake yin tafiyar kilomita mai tarin yawa da kafa don adana abin da ya samu a rana. Game da tallafin gwamnati da ake rabawa, ya ce ba su taba samun ko kwayar hatsi ba.
Fargabar Karuwa Cutar Tamowa A Arewacin Nijeriya
Ko a watan Yunin 2024, sa da kungiyar likitoci ta ‘Doctors Without Borders’ ta bayyana cewa an samu karuwar yara masu fama da tamowa a jihohi 11 da ke Arewacin Nijeriya da suka hada da Borno da Katsina da Sakkwato da Zamfara da Bauchi.
Kungiyar ta bayyana hakan a cikin rahotonta na 2024, inda ta ce an samu yara 1,250 a Jihar Borno kadai da ke fama da tamowa mai alaka da rashin abinci mai gina jiki, wanda ya ninka da kusan kashi dari a wasu yankunan, Arewa adadin da ya zarce na bara.
A cikin sanarwar da ta fitar MSF ta ce: “A cikin makonnin nan an samu gagarumar karuwar a yawan yara masu fama da mummunar cutar rashin isasshen abinci, wadda ke barazana ga rayuwarsu – wadanda ake kai wa asibitocin kungiyar”.
Ta kara da cewa wannan “abin tashin hankali ne idan aka yi kiyasin abin da zai faru lokacin da matsalar za ta kai matukarta a watan Yuli”.
Shugaban kungiyar ta MSF a Nijeriya, Dokta Simba Tirima ya ce: “Tun shekaru biyu da suka gabata muke ta gargadi game da yiwuwar mummunan rashin abinci mai gina jiki. Shekarun 2022 da 2023 sun kasance masu muni, amma abin da zai faru a 2024 ya fi muni”.
Jihohin da aka bayyana a matsayin wadanda matsalar ta fi shafa, akasarin su jihohi ne masu fama da matsalar tsaro.
Borno, inda abin ya fi kamari ta kwashe kusan shekara 15 tana fama da rikicin Boko Haram, lamarin da ya tagayyara kimanin mutum miliyan 2.5.
Wanna matsala ta yi tarnaki ga ayyukan noma da kiwo da harkar kasuwanci.
Mutane da dama sun zama ‘yan gudun hijira, inda aka samar da sansanonin tallafa wa ‘yan gudun hijira a fadin Arewa Maso Gabashin Nijeriya.
Tashin Farashin Kayayyaki
Tashin farashin kayayyaki, musamman na kayayyakin abinci a Nijeriya, ya tirsasa wa dubban ‘yan kasar komawa ga cin wasu nau’oin abincin da jama’a ba su saba da su ba.
A wasu yankuna an samu rahoton mutane kan fita daji inda suke ciro ciyawar ‘rai-ɗore’ suna dafawa sannan sun hada da kuli-kuli su ci domin maganin yunwa.
‘Yan Nijeriya dai suna ta korafi kan irin halin matsi da suka fada ciki, lamarin da ya sa iyalai da dama ba sa iya cin abinci kamar yadda ya kamata.
Sakamakon tsadar rayuwa, al’ummar jihohi da dama a Nijeriya suka yi ta gudanar da zanga-zangar neman dauki daga mahukunta.
Ya zuwa yanzu dai Gwamnatin Jihar Borno, karkashin jagorancin Babagana Umara Zulum ba ta ce komai kan lamarin ba, amma dai gwamnatin tana iya kokarinta wajen ganin ta tallafa wa masu rauni da wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su.
Har wa yau, Zulum ya sha raba wa mutane da masu karamin karfi, kayan abinci da sauran kayan agaji da suke bukata.
A gefe guda kuma akwai kungiyoyin agaji masu tarin yawa da suke taimakawa da kayan agaji a jihar duk da cewar a wasu lokuta suna kokawa kan tallafin da suke samu na yin kadan.
Ko a watan Mayun 2024, sai da Majalisar Dinkin duniya da Gwamnatin Tarayya, suka yi kiran bukatar dala miliyan 306.4 domin magance matsalar tamowa a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe.