Wasu fusattun mutanen garin Dansadau da ke Jihar Zamfara, sun kai wa wani ɗan Majalisar Dokokin Jihar, Kabiru Mikailu, hari a ranar Laraba, bisa zargin cewa ya yi watsi da al’ummar mazaɓarsa.
Ɗan majalisar, mai wakiltar Maru ta Kudu, an kai masa harin ne yayin da yake tare da Gwamna Dauda Lawal a wata ziyara zuwa garin.
- Cikin Sauƙi Na Yanke Shawarar Komawa APC – Gwamna Fubara
- Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Sun Jima Suna Kitsa Karairayi
Mazauna yankin sun zarge shi da rashin zuwa yankin ko kula da halin da suke ciki, duk da hare-haren ‘yan bindiga ke kai wa yankin.
Jami’an tsaro sun hanzarta shiga tsakani domin ceto shi tare da dawo da zaman lafiya.
Gwamna Dauda Lawal ya je Dansadau ne, domin ƙaddamar da aikin gyaran hanyar Dansadau zuwa Gusau, sannan ya sanar da shirin gyaran asibitin Dansadau da samar da wutar lantarki mai aiki da hasken rana.
Daga bisani, Sarkin Dansadau ya karrama gwamnan da sarautar gargajiya saboda ayyukan ci gaba da yake yi a jihar.














