Daga Mubakar Umar, Abuja
Wata daliba a Kwalejin Ilmi da ke Jihar Ondo, mai suna Mary Olaniyan, ta tsallake rijiy da baya, bayan kwashe tsawon kwanaki goma sha daya da ta yi a hannun masu garkuwa da mutane. Inda a gefe guda kuma aka tsinci gawarwakin takwarorinta guda biyu, Blessing da Mary wadanda su ma dalibai ne a wannan Kwalejin ta ilmi da ke Ondo.
Olaniyanne daliba a Sashen Tarihi, ta bayyana yadda wasu maza karti hudu suka yi awon gaba da ita a mota mai fenti tasi bayan fitowarta daga Kwalejin.
“Ni da wata yarinya muka zauna a kujerar gaba kusa da direban tasin, wasu maza su biyu daga cikin fasinjojin motar suka ce za su sauka a Yaba babban birnin Ondo, shiga ta motar ke da wuya na sume, farkawar da zan yi, na gan ni a wani surkukin daji mai ban tsoro.” In ji ta.
“Kubuta ta daga hannun wadannan azzalumai ko masu garkuwa da mutane, wani iko ne da buwaya ta Allah. Don kuwa na samu wannan dama ce a daidai lokacin da sa-in-sa da rikici ya barke a tsakanin su, inda na samu damar arce wa da gudu na shiga cikin dokar daji. Haka na yi ta dannawa cikin wannan daji har sai da na samu kaina a titin Ile-Oluji/Ipetu Ijesa, inda na samu wata yarinya ta dora ni a hanyar zuwa garin Ondo.