Jamila Mamy Janafty, wacce sananniyar marubuciyar yanar gizo ce da ta wallafa littafan Hausa da dama da suka hada da SAIFUDDEEN, TA FITA ZAKKA, GIDANMU da dai sauransu.
Ta karyata rade-radin cewar Allah Ya yi mata rasuwa a ranar Asabar 11/03/2023. Zancen da ya mamaye duniyar rubutu da marubuta cikin kankanin lokaci kamar wutar daji.
- ‘Yan Nijeriya Sama Da Mutane 39 Ne Suka Mutu A Zaben 2023
- Kamata Ya Yi A Yi Hadin Kai Don Magance Kwayar Cutar COVID-19
Marubuciya Jamila, cikin wani gajeren rubutu da ta fitar dai, ta bayyana cewa: ba ma ita ba ce a hoton da ake yadawa da nufin ita ce, asali ma ba ta da alaka da wannan hoton gaba daya.
Ga dai tattaunawar da wakilinmu ADAMU YUSUF INDABO ya yi da fitacciyar marubuciyar bayan da wasu suka kashe ta da fatar baki.
An ce kin mutu har an kai ki kushewa, to yanzu ke ce din ko fatalwarki ce nake magana da ita?
(Dariya) Ni ce nan da kaina ba fatalwa ba, saboda ina nan a raye ban mutu ba. Zuki ta malle ce kawai irin na masu son bayar da labari kuma ba su da abun fada, shi ne suke bigewa da kirkirar karyar cewa wai na mutu. Wanda hakan ba sabon abu ba ne kashe shahararrun mutane da baki, musamman fitattun jaruman fina-finai, da mawaka da kuma marubuta. To ni ma kusan abun da ya faru a kaina ke nan.
To ya kika ji da ana yada hotonki tare da cewar kin rasu?
Gaskiya ni ban ji komai ba, da farko Saboda ban dauka abun zai wuce tunanina ba. Ban zata abun zai yada duniya cikin lokaci kankani ba. Sannan karin abun da ya sa ban tashi hankalina ba shi ne, wannan hoton da suke yawo da shi, ba ni ba ce a cikin hoton. Asali ma ba ni da alaka da wannan hoton gaba daya.
Au hoton wacce aka lika a sanarwar mutuwar taki ke nan ba ke ba ce?
Ai kai ma ka san ba ni din ba ce. To na kara fada ma ni ma da bakina cewa ba ni ba ce, kuma ban san ta ba, ban san ina aka samo hoton ba. Yadda ka gan shi ni ma haka na gan shi.
Kuma ya kika fuskanci mutane da wannan al’amari?
Ai ranar da aka fara yada wannan labarin kanzon kuregen ban san wainar da ake toyawa ba, saboda wayata na kashe ta tun daran ranar da abun ya fara yaduwa. Sai da safe da misalin karfe Goma na safe (10:00AM) na kunna, sai ga wayar wata kawata marubuciya Surayyah Dahiru Gwaram ya fara shigo min tana sanar da ni ita ma ta samu kiran wayoyi ya fi a kirga a kan ana neman tabbacin na mutu ko ina nan da raina? Gaskiya ba ma ni ba hatta kawayena da makusantana sun sha kiran waya da amsa tambayoyin mutane a kan ko na mutun da gaske.
To wanna mataki kika dauka na shelantawa duniya cewar ke fa kina raye?
Na dauki matakin yin write-up gajere mai taken JANAFTY NA NAN A RAYE BA TA MUTU. Kuma na yi status da kaina a WhatsApp, kuma posting a dandalin abokai na facebook. Haka kuma na nemi ‘yan uwa da abokan arziki sun taya ni karyata wannan jita-jitar a shafukansu na yanar gizo. Ga kuma uwa uba wanannan tattaunawa da nake yi da jaridarku mai farin jini, da ita kadai ma ta isa gamsar da duniya cewa, Janafty numfashinta bai kare ba da saura.
Wacce rana abun ya fara yaduwa?
Ranar Asabar ne da yamma. (11/03/2023) saboda a ranar na samu labarin rasuwar daya daga cikin membes din cikin groups dina, sunanta Ummi Hafsah da ta yi hatsari kuma Allah ya yi mata rasuwa. Kuma ko hotonta ba mu fitar ba. To sai na bada sanarwan rasuwan nata a madadin duka members dina. Ina ga daga wannan lokacin ne sai aka sauya labari aka fara yawo da mutuwata,sannan labarin ya cigaba da bazuwa har yau din nan mutane suna ta kira da charts domin tabbatarwa.
To amma kin san shahararrun mutane dama an saba kashe su da baki. A ganin ki me ke kawo hakan?
To zan iya cewa kalubale daman na matakin nasara. Kuma daman ita nasara ba ta zuwa sai da kalubale. To ni dai ina nan da raina ban mutu ba . Wannan abun kuma da ya faru ba zai sauya komai ba, domin daman kowane mai rai wata rana mamaci ne. Sai dai na ce Alhamdulillah ina godiya ga Allah da kuma duka masoyana, na ga kauna, na gode kwarai. Allah ya bar zaman tare har gaban abada. Ameen.