• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

by Idris Aliyu Daudawa
3 hours ago
PDP

Shugaban majalisar Wakilai ta kasa, Honorabul Abbas Tajudeen, ya ce al’ummar Kudancin Kaduna suna tare da jam’iyyar (APC), saboda sun gamsu da irin yadda Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yake tafiyar da lamurran mulkinsa.

Abbas yayi wannan bayanin ne ranar Lahadi a wajen taron amsar dawowar manyan ‘yan siyasa biyu daga Kudancin Kaduna wadanda a shekarun baya suna jam’iyyar (PDP) ne a Kafanchan.

  • Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji
  • Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Wadanda suka sauya sheka dagaThose who defected from the PDP zuwa APC sun hada da Sanatan da yake wakiltar Kaduna ta Kudu, Sanata Sunday Marshall Katung, da kuma mamba mai wakiltar mazabar tarayya ta Jama’a/Sanga, Honorabul. Daniel Amos, tare da dubban magoya bayansu.

Shugaban majalisar, a jawabin da mai ba shi shawara na musamman kan lamurran ‘yan jaridu da wayar da kan jama’a, Musa Krishi yace Shugaban kasa Tinubu ya fifita ci gaban Kudancin Kaduna wajen kawo masu ayyuka a wurin.

Abbas, wanda ya koma baya kwarai da gaske wajen bada tarihi, ya ce, “tun daga shekarar 1999, Kudancin Kaduna wani babban mazauni ne na PDP. Shekaru da yawa da suka wuce, sun yi matukar nuna jajircewa, a dukkanin lamurransu gaba daya. Sai dai kuma kash! halin da ake ciki yanzu duk babu wannan abin ya kare.

LABARAI MASU NASABA

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura

“Mutanen duk sun manta da ‘yan garancin da suka yi gaba dayansu suka shiga wani sabon babi. Babban bango da ake ingina da shi ya fadi. Yanzu Kudancin Kaduna na jam’iyyar APC ne.”

Ya yi bayanin komawar manyan mutanen biyu zuwa APC wani kokarin ci gaba ne na shi Kakakin majalisar, ya ce SHugaban majalisar ya kara jadddad Sanata Katung da Honorabul. Amos “sun zabi lamarin kawo ci gaba ne. Sun zabi su ci gaba da kasancewa da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne da kuma APC. Wannan ba karamin sauya jam’iyya bane. Jirgizar kasa ce ta siyasa. Wani sabon babi ne ga siyasar Kudancin Kaduna, da kuma gaba dayan Nijeriya.”

“’Yan ‘uwana maza da mata wannan sauay shekar wani sako ne, wanda yake nuna lokacin rarrabuwar kai ya kare. Sako ne da yake nuna al’ummar kudancin Kaduna sun shirya tsaf, su kara yin ci gaba saboda ciyar da ci gaban Nijeriya.Sako ne da yake nuna APC yanzu wuri ne na hadin kai, wurin sa kai, da kuma ci gaba.

“Shugaban kasa ya nuna cewar a shirye yake wajen ci gaban Kudancin na Kaduna. Ya saurari kukan da aka dade na yi na kada a manta da su a rika tafiya tare da su, ya kuma yi abinda ya kamata wajen share masu hawaye da, yin ayyukan da suka dace.

“Jami’ar kimiyya ta gwamnatin tarayya da aka yi a Kachia, da wannan mulkin na Tinubu yayi wata manuniya ce mai nuna cewar da akwai fata ta gari da kuma farfado da sha’anin ci gaba. Bada dadewa za ta budewa dalibai hanya domin a fara daidata hanyar data kamata wajen zakulo masu ilimin kimiyya a nan gaba kadan, wadanda za su rika bullo da abubuwan ci gaba da kuma tunanin da me da me suka kamata ayi.

“Kafa Asibitin gwamnatin tarayya a Kafanchan ya nuna cewa gwamnatin ta damu kwarai akan kowa da kowa lamarin kula da lafiyar al’umma. Wajen kawo saukin samun inda za aje domin kulawa da lafiya cikin sauki da kuma daukaka lamarin kula da lafiyar al’umma na Kudancin Kaduna.

“Hakanan ma kafa barikin sojoji a Samarun Kataf wani sabon babi ne na kokarin samar da zaman lafiya da tsaro aka sa a gaba. Yin hakan ya nuna matuka gwamnati ta shirya kamar yadda ya dace wajen kare rayuwar al’umma, da wuraren da suke zama, da kuma kwantar masu da hankali na nuna an damu da tsaron wurin da kwanciyar hakalin al’ummar da suke wurin.

“Duk wadannan suna ganin gaskiya da akwai adalci wajen tunawa da su al’ummar wajen.Hakan ya nuna Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana tafiyar da jagorancinsa na cika alkawari wajen yin abubuwan da suka dace. Shi Shugaba ne mai yin abinda ya yi kuduri a zuciyarsa kawo ci gaba wurin daya dace matuka.”

Shugaban har ila yau ya tabbatar da an sa ko kuma daukar ‘yan asalin wurin wato Kudancin Kaduna wuraren da za su kawo ci gaban wurin ta hanyar la’akari da menene muradin Shugaban kasa akan lamarin da ya shafi wurin.

“An nada Bishop Matthew Hassan Kukah a matsayin jagora kuam Shugaba na wadanda za su jagorancin tafiyar ta jami’ar kimiyya ta gwamnatin tarayya, Kachia. Farfesa Kurid Williams Barnabas shi ne mataimakin Shugaban jami’ar na farko.Wadannan nade- naden wata girmamawa ce ta Kudancin Kaduna. Don haka hakan ya nuna ana lura matuka ga lamarin daya shafi kwarewa da kuma aiwatar da gaskiya.”

Shugaban majalisar Wakilai Abbas yace maganar gaskiya Gwanan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani“a matsayi wani mutum ne da yake bada gudunmawar ci gaba,”inda ya kara da cewa’ “yadda yake tafiyar da lamurran gwamnatinsa tamkar budewa kowa kofa ne ya shigo a tafi tare da shi, saboda ya daidaita kawunan al’umma wadanda a shekarun baya basu ga Maciji da juna. Ya daukaka ci gaba da nuna ya fi duk wani lamarin siyasa da kuma hada kai maimakon, maida hankali kan ita siyasar.”

A kowane lokaci Shugaban majalisa yana yiwa ‘yan kudancin Kaduna a matsayin ‘yan’uwansa ne maza da mata, “Irin soyayyar da yake yiwa yankin ta nuna lamarin ya dade tare da samun ranar cika kudurin. Abokantakar da yake da Shugabannin wurin wani abu ne wanda ya kunshi biyayya da kuma amana da mutunta juna.

“Aiki tare da Shugaban kasa Tinubu, mun tabbatar da cewa kasafin kudin 2025 da aka yiwa shi sashen na Kudancin Kaduna wani sabon babi ne mai nuna lalle ba a manta dasu ba. Kudancin Kaduna yanzu wani wuri ne na ci gaban kasa. Ayyukan da aka yi ba ayi su bane domin saboda yau kadai bane. Tamkar wani zuba jari ne aka yi saboda gaba. Saboda ayyukan za su ilimantar bunkasawa da daukakawa, da kuma samarwa al’ummar yadda za su san mutane domin ai kowa ya san sabo, da Maza ma jari ne saboda gaba.

Ya gode wa Shugaban majalisar Tajudden Abbas saboda yadda yake aiki tare da shi domin tabbatar da ba a manta da kowa ba wajen samar da ayyukan gwamnati, saboda kamar yadda ya ce sun samu nasarori cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jerin Gwarazan Taurarinmu!
Rahotonni

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

November 7, 2025
‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri 4, Sun Ƙwato Makamai A Filato
Labarai

Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura

November 7, 2025
Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki
Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

November 7, 2025
Next Post
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

LABARAI MASU NASABA

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
APC Da Uba Sani Ba Su Lashe Zaben Gwamnan Kaduna Ba -PDP

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

November 7, 2025
Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

November 7, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu!

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

November 7, 2025
‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri 4, Sun Ƙwato Makamai A Filato

Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.