Daga Idris Umar,
A ranar laraba ta wannan makon da muke ciki lokaci ne ya yi halin sa, yadda kuma hakan ya gigatawa matasa da kuma sauran al’ummar garin Samarun Zariya cikin karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna, hankali inda aka samu rasuwar wani sananne kuma shahararren matashi wanda yake cikin gabar lokacinsa na rayuwa.
Wannan matashi ba wani bane illah Bashir Maiwada da aka fi sani da (Leck Over) wato daya daga cikin masu taimakawa shugaban karamar hukumar Sabon Gari Honorabul injiniya Muhammad Ibrahim, a sashen hulda da jama’a da kuma sauran ayyukan cikin gida.
Bashir ya rasa ransa ne a sanadiyar wata gajeruwar rashin lafiyar da ya yi fama da ita.
Bashir ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya.
Rasuwar matashin ta firgita matasan garin Samaru da kuma karamar hukumar Sabon Gari baki daya, bama kamar idan aka yi la’akari da irin irin kyawawan dabi’un shi matashin.
Wakilinmu LEADERSHIP A Yau Juma’a ya ziyarci taron addu’ar kwana uku wadda ta gudana a kofar gidan shi marigayin da ke layin mangwarori Hayin Dogo Samaru Zariya.
Bugu da kari kuma duk wani mai fada a ji a karamar hukumar ta Sabon Gari ya zo saboda ya jajantawa shi shugaban karamar hukumar.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin wasu daga cikin abokan marigayin dangane da halayen shi mamacin kafin rasuwar tasa.Malam Sasino shi ne abokinsa na kud da kud a shekaru masu yawa don haka ne ma ga abinda ya ce,’’Allah ya dauki ran abokina, dan‘uwana a daidai lokacin da nake bukatarsa domin halayensana kirki.
Malam ya kara da cewar halayen Bashir Leck Ober abin ayi koyine ga duk wani matashin dan siyasa a karamar hukumar Sabon Garin don haka muna yi masa fata samun rahama a makwancinsa.
Alhaji kwalabe daya daga cikin masu taimakawa shugaban karamar hukumar a bangaren siyasar shi dare da harkokin cikin gida shima cewa ya yi, ‘Hakika mun yi rashi, domin kuwa shi mamacin ya kasance mai kula da aikinsa, mai mutunta jama’a, da kula da alkawari a yanzu samun mai hakuri da cika alkari irinsa a gaskiya sai antona bisa haka muna bika salon ta’aziyya ga dukkan yan’uwa da abokan arzuki rate da kira ga matasa da cewa ya kamata rasuwar Bashir Leck Ober yazan aya a garemu ta hanyar koyi da halayansa muna rokon Allah ya kyautata makwancinsa’’.
Shi kuwa Malam Muhammad Auwal Nasri wanda aka fi sani da( Gafatta ) masanin kimiyyar gine- gine, kuma dan kwangila, wanda shi aboki ne ga shugan karamar hukumar ta Sabon Garin shi ma cewa ya yi rashin Bashir wani gibi ne wanda zai yi wuyar cikewa don haka ne, yayi fatar Allah ya yi masa gafara, kuma Allah ya albarkaci zuruyar daya bari.
Shi ma shugaban karamar hukumar ta Sabon Gari, Injiniya Muhammad Usman, wanda ya ke cike da alhinin da kuma jimamin ita rasuwa ya bayyana irin halayen kirki na shi mamacin, wanda ya nuna cewar rasuwar sa babban al’amari ne mai tada hankali, ya kuma roki wadanda suke mu’amala da Bashir Leck Ober da cewar su yafe masa dukkan laifin da ya yi masu a matsayinsa na abokinsu.
Tun kafin rasuwar tasa matasan suka nuna sun shirya tsaf don goya mashi baya don fitowa takara daga ko wacce jam’iyya ce ya tsaya takara saboda kwarewarsa a bangaren wajen mu’a mulla da al’ummar wurin.
Yanzu haka jama’a ne suke cigaba da yin tururuwa zuwa wajen gabatar da sakon ta’aziyyarsu ga mai girma shugaban karamar hukumar Sabon Garin tare da yi masa fatar ya samu rahamar Allah.Bashir Leck Ober ya rasu ya bar matarsa kaya tare da yara. Allah ya jikansa yasa ya huta amin.