Matashin nan da, mai kabu-kabu da Keken Adaidata Sahu (Keke Napep) da ya tsinci Naira Miliyan 15 na wasu ‘yan kasar Chadi da suka manta a kekensa ya mayar ba tare da bacewar kobo ba, ya bayyana yadda rayuwarsa ta sauya tun bayan wannan lamari.
A zantawarsa da LEADERSHIP Hausa, yayin bikin karrama shi a matsayin Gwarzon Matashi na Kamfanin LEADERSHIP a 2023, ya bayyana cewa ya fahimci aikata gaskiya na sa kwanciyar hankali da natsuwa a rayuwar mutum, tare da ci gaba.
- Babban Taron LEADERSHIP Ya Zakulo Yadda Za A Ceto Nijeriya
- Kano Za Ta Haɗa Gwiwa Da Afrinvest Don Haɓɓaka Kasuwanci Da Ci Gaban Jihar
Daga cikin sauyin da ya samu na rayuwa, ya bayyana cewa a da ba ya karatu domin ya bar makaranta saboda iyayensa ba su da karfin biya masa amma yanzu ya samu hanyoyi da damarmaki na karatu sai wanda ya zaba.
Har ila yau, a baya keken da yake kabu-kabu da shi ba nasa ba ne, taba-ka-lashe yake yi, amma yanzu ya mallaki kekensa na kansa da yake aiki da shi bayan ya dawo makaranta domin taimaka wa iyayensa.
Hatta ma abin da ya shafi tufafin sawa yanzu ba shi da matsala ko kadan, sai wanda ya zaba, yake saya ya sa duka albarkacin biyayya ga iyaye da aikata gaskiya.
“Ta dalilin wannan al’amari a matsayina na ba kowa ba a da, yanzu an ba ni matsayin Jakadan matashi na Kungiyar Dattawan Arewa. Ana misali da ni a wurare da dama domin karfafa wa sauran matasa. Ina yi wa Allah godiya da wannan baiwar. Har yanzu dai, a da muna hayar gida ne, inda muke biyan haya da kyar, amma yanzu na saya wa iyayena gida inda suka koma da zama cikin kwanciyar hankali.”
Bugu da kari, Auwalu ya lura da cewa, wurare da manyan mutane ke zuwa da bai taba tunanin zai je ba, yanzu a haka neman shi ma ake yi ana karrama shi baya ga damammaki ta ganawa da manyan mutane da dama da bai taba yi tunani ba a da. Kuma duk inda ya je suna karrama shi.
Yanzu haka a ranar talatar makon nan, ya samu lambar yabo ta zama gwarzon matashi na Kamfanin LEADERSHIP a shekara ta 2023 bisa gaskiyar da ya nuna wadda ta zama bar koyi a tsakanin matasan kasar nan da galibi ake wa Kallon marasa tarbiyya.
“Wannan lambar yabo ta dadada mini rai sosai, inda aka sanya ni cikin jerin manyan mutane da suka hada da gwamnoni, wakilin shugaban kasa, manyan ‘yan kasuwa, manyan yan boko da sauransu”
Bayan an mika masa lambar yabo ne, sai wasu kofofin alherai suka sake bude masa, yayin da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi ya sanar da daukar nauyin karatunsa a daya daga cikin jami’o’i mafi tsada a Abuja (Jami’ar Baze) har zuwa kammala digiri na farko.
Wakazalika, bayan sanar da daukar nauyin karatun ne, sai Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, cikin wani yanayi na nishadi a zauren bikin, ya ce Peter Obi ba zai yi wa APC yankan baya ba, don haka ya sanar da tallafin Naira Miliyan 250 daga bangaren shugaban kasa, gwamnoni, ministoci, shi kansa da kuma Jihar Neja kanta, kana ya yi alkawarin Sanya wa daya daga cikin hanyoyin da yake ginawa a Neja sunan Auwalu.
…Tarihin Rayuwarsa A Takaice Da Burinsa Na Rayuwa
“Sunana Auwalu Salisu, direban Adaidaiata Sahu, mutumin Kano, na yi makarantar Firamare ta ‘Yankaba na je makarantar Sakadare ta Kawaji amma bangaren maza amma ban kammala ba saboda rashin kudi, sai na daina zuwa makaranta na fara da yin yaron mota. Sai na bari na koma direban Adaidaita Sahu (Keke Napep). A lokacin wanda nake tukawa ba nawa ba ne na abokina ne.
“Na hadu da mutumin da ya manta da kudinsa a Keke Napep da nake tukawa wata rana da safe, na shiga Badawa Layout ne na zo wucewa sai ya ce na tsaya, na tsaya, sai ya ce ya lura ina da hankali, su uku ne da buhu a gabansu sai suka ce mani zan kai su Tafawa Balewa, suka ce mani me za su ba ni? Na ce su ba ni 500 sai daya ya ce za su ba ni 300. Sai daya daga cikinsu ya ce su hau kawai muje, da suka shiga sai suka sa buhun nasu a bayan mashin, da muka isa Tafawa Balewa sai suka manta da buhun a baya saboda suna ta surutu. Bayan da na baro Tafawa Balewa sai na ga buhu a bayan mashin, ina zuwa sai na bude buhun sai na ga ai kudi ne a ciki, daga nan sai na yi maza- maza na tafi gida na nuna wa Mamarmu ta ce in je in samu Babanmu in nuna masa.
“Dama shi ma a rawun din yake sayar da nama, na same shi na gaya masa sai ya kira yayansa ya fada masa abin da yake faruwa, sai ya ce mu je ga yayan nasa domin a samu mafita, sai aka ce na koma wurin da na dauko su. Na koma, na zagaya, na zagaya ban gan su ba, na zo na gaya masu ban gansu ba sai Babana ya ce mani yanzu ya za a yi, ko za mu je wurin ‘yansanda ko kuma mu je gidan Rediyo sai na ce ma shi a’a ai kudin suna da yawa. Gara a je gida a aje su a ci gaba da neman masu su, sai Babanmu ya gaya wa Mamarmu wadannan kudi a ajiye su har Allah ya sa a ga masu su a mayar masu.
“Ta dauko ta ajiye su, bayan kwana daya ba a ji wani labari ba sai a kwana na biyu da safe Mamarmu tana sauraren Rediyo sai ta ji a Rediyon Arewa ana cigiya, sai ta sa aka kira ni ta ce ga nambar waya an ba da, ga shi in kira, dama nambobin biyu ne sai na dauko waya na kira, na kira har sau uku amma ba a daga ba, to sai na kara kira, ina kira mutumin yana dagawa sai ya fara fada, sai na ce ma sa direban mashin ne. Daga nan kuma sai ya fara gaida ni, ya ce don Allah ina nake, na ce ma shi ina ‘Yankaba, ya ce ya za a yi ya zo mu hadu ni kuma na ce ma shi a’a, sai dai mu hadu a Rediyon Arewa tun da can ne suka yi cigiya, sai ya ce ai ba wani abu ba ne sai su ba ni wani abu. Ya ce za su ba ni wani abu su amshi kudinsu ni kuwa na ce mashi mu hadu a can din dai. Sai muka hadu a gidan Rediyon Arewa aka dauki kudinsu aka ba su, ka ji yadda abin ya faru.”
Da aka tambaye shi abubuwan da suka biyo baya, Auwalu ya ci gaba da cewa, “Gaskiya na samu kudi Alhamdu lillahi har an sai mani sabon mashin wannan nawa ne kuma har yanzu ina hawa mashin”, dangane da ‘yan matan da aka masa tayin ya aura kuma ya ce, “gaskiya wani ya kira ni daga wani wuri ya ce mani shine shugaban dalilin aure, ya ce na je akwai ‘yan mata in zaba za a daura mani sai na gaya ma shi ni gaskiya ban tashi yin aure ba.”
To, ko me ya sa duk da Auwalu da iyayensa talakawa ne lokacin da ya tsinci kudin amma kuma ya mayar, ya ce, “Maganar gaskiya dukkannin wadansu al’amuran rayuwa sai mun danne zuciyarmu sannan mu yi hakuri da duk irin halin da mutum ya tsinci kansa.”
Da aka tambaye shi abin da yake da burin zama a rayuwa nan gaba, Auwalu, ya ce, “Ni ina da burin in zama ma’aikaci, ina son in zama Dansanda saboda ni dama ra’ayina kenan. Gaskiya saboda irin wulakanci da ma’aikata ke yi kamar cin hanci da rashin mutunci, ina son na yi iya kokarina wajen kawo gyara a kan haka, kuma ina kira ga sauran jami’ai duk a hadu a gyara baki daya.”