Nasir S Gwangwazo" />

Yadda Rikita-rikitar Magu Ta Wakana

A wayewar garin jiya da rana ne rahotanni su ka fantsama duniya cewa, jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun cafke Shugaban Riko na Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) na kasa, Ibrahim Magu, bisa zarge-zargen da ke da alaka da cin hanci da rashawa a wani yanayi da a ke yi ma sa kallo a matsayin dara ta ci gida ko kuma mai dokar bacci ya bige da gyangyadi.

Tun a kwanakin baya ne dai a ke ta rade-radin cewa, za a kama Magu sakamakon wani mummunan rahoto da Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayyar Nijeriya, Abubakar Malami (SAN) ya aike wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya na mai zargin Magun da aikata wata badakala da ke da alaka da kudaden da hukumar ta amso daga wadanda a ke zargi ko tuhuma ba tare da an mayar da su inda yakamata ba, sannan kuma da zargin shugaban da nuna taurin kai da jin kai ga na gaba da shi, inda ya ke kin yin biyayya ga ofishin ministan, duk da cewa, a karkashin kulawar ma’aikatarsa hukumar ta EFCC ta ke.

Daga bisani Shugaba Buhari ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan batun, don tabbatar da gaskiyar lamarin da kuma daukar matakan da su ka dace. Wannan ne ya sa a ka kafa kwamitin bincike a karkashin kulawar Fadar Shugaban Kasa, don yin abinda ya fi dacewa.

Wasu rahotanni sun nuna cewa, jami’an DSS sun yi dirar mikiya ne jiya a kan shugaban hukumar, inda su ka damke shi kuma su ka yi awon gaba da shi nan take.

To, sai dai kuma nan da nan hukumar DSS ta bayar da sanarwar cewa, ko kusa ba ita ce a aikata wannan aiki ba. A takaice ma dai ba ta da masaniyar cewa, jami’anta sun aikata wani abu makamancin hakan kan Malam Magu.

A wata sanarwa ga manema labarai mai dauke da sa hannun Jami’in Yada Labarai DSS, Peter Afunanya, a jiyan, hukumar ta ce, “tuni an damu hukumar da tambayoyi kan zargin kama Magu, inda kuma lamarin ba shi da alaka da hukumarmu.”

To, shi ma a yayin da a ka tuntubi Jami’in Kula da Kafafen Yada Labaran Magu, wato Tony Amokeodo, ya ce, ba kama maigidan nasa a ka yi ba, illa dai kawai ya amsa gayyatar kwamitin Fadar Shugaban Kasa ne.

Ita ma EFCC, ta hannun Kakakinta, Mr Dele Oyewale, ta bayar da sanarwa a jiyan cewa, kwamitin na Fadar Shugaban Kasa ya na zamansa a zauren taro na Bankuet Hall da ke cikin fadar ne a jiyan, inda ya gayyaci shugaban hukumar, domin bayar da ba’asin ayyukan EFCC din da a ke neman karin bayani a kai.

“An gayyace shi ne a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa hedikwatar ’yan sanda ta kasa da ke Abuja, don gudanar da wata ganawa. Don haka ba kama shi a ka yi ba, kuma ba tilasta ma sa a ka yi ya amsa gayyatar ba. Kuma ya na tare da daya daga cikin ’yan tawagar kula da sashen shari’a na hukumar a lokacin da ya halarci zaman kwamitin na musamman,” in ji sanarwar ta Oyewale.

A yanzu dai an zuba idanu a ga yadda za ta wakana, musamman kasancewar a yanzu wanda a ke kallo a matsayin mai tsaya wa Magu a fadar gwamnatin, wato tsohon Shugaban Ma’aikatan fadar Shugaban Kasa Marigayi Abba Kyari, ya rasu, inda a lokacin da ya ke raye a ke ganin wasu manyan jami’an gwamnatin su na takun saka da Magu, amma sun kasa galaba kansa ne, saboda kasancewar ya na da daurin gindin Marigayi Kyari.

Exit mobile version