Masana sufurin jiragen sama sun bayyana yadda suke ganin rufe sararin samaniyar Nijar zai shafi wasu daga cikin kasashen Yammacin Afirka da ita kanta Nijar ta hanyoyi da dama.
Dangantaka tsakanin Jamhuriyar Nijar da kungiyar ECOWAS da wasu kasashen Yamma na kara tsami sakamakon kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum da sojoji suka yi, lamarin da ake fargabar zai iya jefa yankin Sahel cikin karin rikici.
- Gwamnatin Tarayya Ta Janye Karar Da Ta Shigar A Kan NLC Kan Shiga Zanga-zanga
- Alkaluman Hidimar Cinikayya Ta Yanar Gizo Na Sin Sun Karu a Watan Yuli
A ranar Lahadi da dare ne sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar suka sanar da rufe sararin samaniyar kasar, abin da ke nufin jirage ba za su iya shawagi ko kuma wucewa ta Nijar ba.
Sun dauki matakin ne bayan sun yi zargin cewa kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), na shirin kai wa kasarsu hari bayan wa’adin da ta ba su na mayar da Bazoum kan mulki ko su fuskanci karfin soji ya wuce.
Ana fargabar rufe sararin samaniyar za ta sa jirage su rinka yin zagaye lamarin da zai iya haifar musu da sabbin kalubale.
Masana sufurin jiragen sama sun bayyana yadda suke ganin rufe sararin samaniyar na Nijar zai shafi wasu daga cikin kasashen Yammacin Afirka da ita kan ta Nijar.