ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Sha’anin Noman Abarba Ke Taimakawa Kyautata Zaman Rayuwar Mazauna Wasu Kauyuka A Kasar Sin

by CGTN Hausa
2 years ago
Abarba

Kwanan baya, na ziyarci kauyen Yugonglou na gundumar Xuwen dake birnin Zhanjiang na lardin Guangdong, wurin da ya shahara da noman abarba a kasar Sin. Yayin da na shiga gonakin abarba marasa iyaka, na gano dalilin da ya sa ake yiwa gonakin take da “Tekun abarba”. Mazauna kauyen dake kokarin girbin abarba sun gaya min cewa, dukkanin mazauna kauyen suna ayyuka masu alaka da abarba, don haka ana iya cewa, a kashin kan ta abarba na kawo arziki ga wannan kauye.

Alkaluman da aka samar sun shaida cewa, a shekarar 2023, fadin gonakin da aka shuka abarba a gundumar Xuwen ya kai fiye da hekta dubu 22, kuma yawan abarba da aka samar ya zarce ton dubu 788, yayin da kudin da aikin ya samar ya kai sama da dalar Amurka miliyan 751. Inda ya taimaka wajen samar da guraben aikin yi dubu 146. Ana jigilar abarba da aka girba daga gonaki zuwa kamfanonin sarrafa ta iri daban-daban, daga baya suna shiga kasuwannin cikin gida da na waje.

  • Kasar Sin Ta Soki Zargin Da Philippines Ta Yi Mata Na Gina Tsibiri A Kusa Da Sashen Tudun Ruwa Na Xianbin Jiao
  • Kenya: An Kammala Baje Kolin Harkokin Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Afrika

Amma, a shekarun baya can, mazauna gundumar Xuwen masu shuka abarba, suna takaicin rashin sayar da su, har sun rube a gonaki. Da ganin hakan, gundumar Xuwen ta gaggauta raya kanta bisa shirin gwamnatin lardin Guangdong na raya ingantattun birane da gundumomi da kauyuka, inda ba ma kawai ta kafa cibiyar samar da alkaluma dake ba da taimako ga manoma wajen zabar nau’o’in abarba da tabbatar da farashinta da sauran bangarori ba, har ma da gaggauta raya sha’anin yawon shakatawa dake da alaka da al’adun abarba.

ADVERTISEMENT

Ta haka, na shiga otel din da aka gyara bisa gidajen mazauna kauyen, inda na ga gonakin abarba marasa iyaka, tare da jin kamshin abarba. Ba shakka yadda ake raya sha’anin yawon shakatawa mai alaka da al’adun abarba za ta kara kudin shigar mazauna kauyen.

An ce, ko wadanne abarba uku da aka samar a nan kasar Sin, daya daga cikinsu asalin Xuwen ce. Na debi wani na dandana, ruwan abarba mai zaki ya fito nan da nan, kamshi na cike da baki na, abin da ya alamanta zaman rayuwa mai zaki ta jama’ar wannan kauye. (Mai zana da rubuta: MINA)

LABARAI MASU NASABA

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow
Daga Birnin Sin

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Amurka

Gwamnati Ta Dakatar Da Harajin Tsaron Intanet Kan Hada-hadar Kudade

LABARAI MASU NASABA

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.