Kungiyar marubuta ta arewacin Najeriya ‘Nigeria Northern Writers Forum’ ta shirya taron marubutan arewa domin lalubo hanyoyin da za a magance matsalar tsaro a yankin arewa da ma ƙasa baki ɗaya.
Taron na bana, anyi masa take da Amfani da rubuce-rubucen adabi da harsuna a matsayin makamin yaki da matsalar tsaro a yankin arewa da Najeriya baki ɗaya.
Kazalika masana da masu sharhi akan tsaro sun gudanar da ƙasidoji daban-daban da suke da alaƙa da hanya mafi sauki wajan tunkarar matsalar tsaro.
Tun da farko da yake jawabin maraba shugaban kungiyar marubuta Arewacin Najeriya, Dakta Bishir Abusabe ya yi ƙarin haske akan taron na bana wanda ya ce an taɓo batun matsalar da ta addabi yankin arewa.
Ya ce taron zai kasance wani ɗan ba na ƙarfafa gwiwar marubuta saboda irin gudunmawar da suke badawa wajan haɓaka harsuna da adabi.
“Mu anan jihar Katsina muna alfahari da manyan kuma sananun marubuta irin su Abubakar Imam da sauran su, saboda ƙoƙarin da suka yi wajan samar adabi da zai amfani wannan al’umma shekaru da dama masu zuwa.” Inji shi
Dakta Bishir Abusabe ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari musamman irin tallafin da take ba marubuta da harkar rubutu a jihar Katsina.
Shima a nasa jawabin Ferfesa Saleh Abdu wanda ya gabatar da ƙasida akan hanyoyin da ya kamata a bi ta hanyar amfani da adabin gargajiya wajan magance matsalar tsaro a arewacin Najeriya da ma ƙasa baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa adabi hanya ce mafi sauki wajan isar da sako musamman a yanayi da kuma tsari irin na Hausa Fulani da kuma Malam Bahaushe.
Da yake jawabi a wajan taron gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya yaba da ƙoƙarin marubuta wajan bunƙasa al’ada acikin al’umma domin isar da muhimmin sako akan wani al’amari kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
- Nijeriya Ba Za Ta Bunkasa Ba Sai Da Ingantacciyar Wuta – Tambuwal
- IAEA: Za A Tattauna Batun Hadin Gwiwa Tsakanin Amurka Da Birtaniya Da Australiya
Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan yaɗa labarai, al’adu da harkokin cikin gida, Alhaji Abdulkarim Yahaya Sirika ya jadadda aniyar gwamnati wajan haɗa hannu da kungiyar marubuta ta arewacin Najeriya wajan ciyar da ilimi gaba.
Haka kuma ya bayyana cewa daman gwamna Aminu Bello Masari ya ɗauki harkar ilimi a matsayin lamba ɗaya tun zuwan gwamnatin sa, ya ƙara da cewa kungiyar marubuta suna da rawar da za su taka wajan cimma nasarori a tsare-tsaren gwamnati.
” Gwamnatin mu zata cigaba da haɗa hannu da kungiyar marubuta wajan ƙara inganta hanyoyin samar da ilimi a jihar Katsina sannan ya yaba da ƙoƙarin marubuta akan samar da litattafan nazari da bincike ga ɗaliban ilmin.”
Daga ƙarshe ya jaddada goyon bayan gwamnatin jihar Katsina na cigaba da taimakawa marubuta da rubutu a matsayin wani kaso na gudunmawar gwamnatin jihar Katsina.
Wasu daga cikin waɗanda suka gabatar da ƙasida a wannan taron sun haɗa da Ferfesa Saleh Abdu na jami’ar Gwamnatin Tarayyar da ke jihar Gombe da Ferfesa Idris Amale da tsohon shugaban kungiyar Malam Muhammad Kabir Sani da fitaccen mawaki Aminu Abubakar Ladan (Alan Waƙa)
Sannan an gabatar da bada kyaututukan girmamawa ga wasu fitattun mutane da suka haɗa da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da sauran jama’a.