Wata mata a Kasar Amurka mai suna Dorothy Fedeli, ta auri kanta shekara 50 bayan mutuwar aurenta.
Matar ta ce “Na iya kokarina amma na kasa, to me ya sa ba zan auri kaina ba?” Kamar yadda ta fada kafin sanar da auren.
- Shawarar Da Shugabar Cibiyar Kasuwanci Ta Duniya Ta Bai Wa Sabbin Gwamnoni
- Saraki Ga Gwamnoni Masu Barin Gado: Ku Guji Katsaladan A Mulkin Wadanda Suka Gaje Ku
Dorothy Fedeli, mai shekaru 77, ta auri kanta ne a wani bikin iyali da aka yi jihar Ohio na Amurka.
Wani abin mamaki shi ne amaryar ta yi aure shekaru 50 da suka gabata, kuma bayan rabuwar auren ne, ta sha alwashin ba za ta ƙara aure ba.
Dorothy dai na da ‘ya’ya uku da kuma jika daya.
An ga matar sanye da fararen kaya tare da rike furanni a hannunta.
Daurin auren ya samu halartar ‘yan uwa da kuma abokai.
Ta ce ra’ayin auren kanta ya zo mata a lokacin da take cikin coci.
“Today.com” ta ruwaito cewa ta shafe shekaru 40 tana zama ita kadai, kuma ta yanke shawarar yin wani abu na musamman da kanta.
Fedeli ta ce tana cike da annashuwa kamar kowace amarya a ranar aurenta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp