• English
  • Business News
Friday, October 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda ‘Yan Kasuwar Kwari Ke Tafka Asara Saboda Ambaliyar Ruwa A Kano

by Sadiq
3 years ago
Kwari

‘Yan kasuwar Kantin Kwari a Jihar Kano sun koka kan asarar dukiyoyi da suka yi sakamakon ambaliyar ruwa.

Wannan na dauke me cikin wata tattaunawa da LEADERSHIP Hausa ta yi da ‘yan kasuwar, inda suka ce ‘yan kasuwa da dama suna kwashe kayayyakin da ke shagunansu.

  • Masarautar Bwari Jiya Da Yau
  • Dannau Ba Matsalar Aljanu Ba Ce, Aikin Kwakwalwa Ne -Dakta Maryam (Adon Gari)

Rahoton ya nuna cewa, ambaliyar ta afku ne bayan da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a daren ranar Laraba, yayin da aka toshe mafi yawan magudanan ruwa a kasuwar.

Wasu daga cikin ‘yan kasuwar da suka zanta da wakilinmu, sun danganta lamarin da rashin magudanan ruwa, da gina hanyoyin ruwa da kuma sabuwar gadar sama da aka gina a kusa da kasuwar.

Sun yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki domin sun yi asarar kayayyakin na miliyoyin Naira.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule

Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

Kwamared Balarabe Tatari, shi ne shugaban kungiyar ‘yan kasuwa kanana da matsakaita na kantin kwarin, ya yi magana kan yadda suka yi hasashen faruwar irin wannan yanayi a lokacin da aka gina sabbin gine-gine a layin Ta’anbo da kuma layin Bayajidda.

Ya ci gaba da cewa, duk kokarin da kungiyar ta yi don ganin an yi wani abu game da lamarin ya ci tura. Ya ce rashin tsarin sufuri da hanyoyin ruwa a cikin kasuwar ya taimaka wajen ambaliya da sauran haduran muhalli.

Alhaji Balarabe ya bukaci gwamnati da masu ruwa da tsaki da su taimaka wa wadanda abin ya shafa tare da daukar matakin da ya dace domin dakile faruwar lamarin nan gaba.

A halin da ake ciki, shugaban hukumar da ke kula da Kantin Kwari, Alhaji Abba Muhammad Bello ya musanta cewa gine-ginen sun toshe hanyoyin ruwa.

Ya ce an rufe wasu magudanun ruwa ne na wani dan lokaci saboda aikin da ake yi a kasuwar.

Ya jaddada cewa hukumar za ta mika cikakken rahoto ga gwamnati domin daukar matakin da ya dace.

Idan za a iya tunawa, a watan Agustan 2021, ‘yan kasuwa a kasuwar Kantin Kwari sun gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin gamsuwarsu da wani gini da ake ginawa a Layin Ta’anbo a cikin kasuwar.

Sun yi nuni da cewa layin Ta’anbo na daya daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen safarar kayayyaki a cikin kasuwar sannan tasha ce da ke hada magudanun ruwa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu
Labarai

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule

October 24, 2025
Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa
Manyan Labarai

Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

October 24, 2025
Manyan Labarai

Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

October 24, 2025
Next Post
hadeja

Mai Martaba Sarkin Hadeja Zai Cika Shekara 20 Kan Karaga

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule

October 24, 2025
Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

October 24, 2025

Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Sheriff Oboreɓwori: Gwamnan Da Ya Ginu Kan Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaban Al’umma

October 24, 2025
An Kafa Cibiyoyi 296 Na Koyon Fasahar Zamani A Faɗin Nijeriya

An Kafa Cibiyoyi 296 Na Koyon Fasahar Zamani A Faɗin Nijeriya

October 24, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC Uku Da Wasu

Ƴan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC Uku Da Wasu

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

October 24, 2025
Nnamdi Kanu Ya Sake Bayyana A Kotu Ba Tare Da Lauya Ba, Zai Kare Kansa Da Kansa

Nnamdi Kanu Ya Sake Bayyana A Kotu Ba Tare Da Lauya Ba, Zai Kare Kansa Da Kansa

October 24, 2025
Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan ₦2.3 Ga Tsofaffin Ma’aikata Da Iyalansu

Ƙungiyoyin Ma’aikatan Jihar Kaduna Sun Yabawa Gwamna Sani Kan Amincewa Da Sabon Albashin  Ma’aikata

October 24, 2025
Ƙarfin Niyyar Manzon Allah (SAW) Da Matakinsa Na Aƙlul A’ala

Ƙarfin Niyyar Manzon Allah (SAW) Da Matakinsa Na Aƙlul A’ala

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.