Wata ƙungiya mai suna BudgIT da ke sa ido kan yadda ake amfani da kuɗin gwamnati a Nijeriya ta ce wasu ‘yan majalisar dokoki na suna cusa wasu ayyuka marasa amfani cikin kasafin kuɗi.
Rahoton BudgIT ya bayyana cewa an saka kwangiloli har 11,122 a kasafin kuɗi na shekarar 2025, waɗanda za su lashe kuɗi har naira tiriliyan 6.93, ba tare da cancanta ko amfani kai tsaye ga jama’a ba.
- ‘Yansanda Sun Tarwatsa Wuraren Haɗa Jabun Taki A Bauchi, An Cafke Mutum 5
- Kotu Ta Soke Umarnin Kwace Filin Asibitin Tiamin, Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Diyyar ₦2.6bn
Wasu daga cikin waɗannan ayyuka sun haɗa da rabon takin zamani, bayar da tallafin karatu, gina cibiyar koyar da kwamfuta (ICT/CBT), da sayen motoci na tsaro, duk da cewa ba su da alaƙa da aikin ma’aikatar da aka sanya su a cikinta.
BudgIT ta ce waɗannan ayyuka da aka cusawa kasafin kuɗi sun kai kashi 12.5 cikin 100 na duk kuɗaɗen kasafin kuɗin Naira tiriliyan 54.99 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da su.
Ƙungiyar ta ce wannan ɗabi’a tana rage tasirin kuɗin gwamnati, tana kuma sa jama’a rasa amana da gwamnati.
BudgIT ta buƙaci gwamnati da ta riƙa bin gaskiya da adalci wajen tsara kasafin kuɗi, domin a tabbatar kuɗin gwamnati na yi wa jama’a amfani kai tsaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp