Wasu rahotanni sun bayyana cewa ‘yan uwa da makusantan wadanda suka kubuta daga hannun ‘yan bindigar da suka sace su a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, sun biya kudin fansa Naira miliyan 800.
Tun farko an alakanta harin da Boko Haram ko ISWAP, wasu kuma na zargin ‘yan bindiga ne.
- Bukukuwan Babbar Sallah: Wane Tanadi Matasa Suka Yi?
- Zabar Mataimaki: Tinubu Ya Watsa Wa Gwamnonin Arewa Maso Yamma Kasa A Ido
Shi kuma Muhammad Abuzar wanda mutumin kasar Pakistan, ya kubuta ne bayan an biya Naira miliyan 200 a kansa, kudin fansarsa ya fi na kowa.
Majiyar ta ce ‘yan ta’addan sun karbi Naira da kuma Dalar Amurka miliyan 200 kadai aka karba a kudin Naira, an biya sauran miliyan 600 cikin Dalar Amurka.
‘Yan uwan mutanen sun zargi gwamnatin tarayya da yin watsi da halin da ‘yan uwansu ke ciki, don haka suka saida kadarorinsu domin su tara kudi.
Shi ma wani wanda abin ya shafi dan uwansa, ya ce gwamnati ba za ta damu idan an kashe mutanen da aka dauke ba, hakan ta sa dole suka nemi kudin fansarsu.