Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirinmu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai kawo muku yadda za ku magance kyasbi
Mene ne kyasbi? Ya kuma ake magance shi hanyar amfani da magungunan gargajiya a gida?
Kyasbi dai ciwo ne da ya shafi fatar jikin mutum, sannan ba kasafai mutane ke warkewa ba idan sun kamu da shi.
A yau za mu bayyana wa masu karatu wasu hanyoyi ko magungunan gargajiya hudu da za su taimaka wa masu dauke da wannan cutar ko kurajen fuska.
Domin magance matsalolin da suka shafi fata, wadanda suka hada da kyasbi, Makero da kurajan fuska, wadanda an yi-an yi abin ya ci tura, to kun zo wurin da ya dace matukar da gaske kuke wajen son kawar da su.
Abubuwan da za ku tanada:
Man Zaitun, man Kwakwa, Alo bera, Ma’u Khal:
Yadda za ku hada maganin
Man Zaitun da Man Kwakwa:
Bayan kun samu duk wadancan abubuwan da muka ambata a sama, sai ku dauki wannan Alo bera ku saka ta a turmin daka mai tsabta sai ku dan daka ta, ko kuma a sabata.
Lokacin da ake dakawa ko sabawa sai ku rika zuba ruwan Khal kadan-kadan haka, amma kada a saka ruwan sosai ta yadda za ta kwabe ta yi ruwa. Idan kin gama dakawa sai ki samu wata roba mai kyau ki zuba man Zaitun da man kwakwa a ciki ki juya sosai, ana bukatar bayan an juya su, sai a kai hadin a rana mai dan zafi na kamar tsawon awa daya, domin ya yi dan dumi.
Bayan nan za a samu mataci wanda za’a tace mayukan domin a cire itatuwan Alo beran, sannan sai a rika shafa wannan hadin safe da dare idan za’a shiga barci.
InshaAllahu, idan mutum ya hada wadannan abubuwa daidai kamar yadda aka zayyana su a nan zai yi wa Allah godiya, kuma ya yi wa Arewa Times Hausa addu’a. Allah ya sa mu dace.