Kamar kowanne mako wannan shafi ya kan zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma daga bangarori daban-daban. Inda tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin sirikai (Iyayen miji) suke saka ido a kan matan ‘ya’yansu maza.
Musamman ta yadda suke ganin yaran nasu na kyautatawa matansu na hakkokin daya rataya a wuyansu, wanda kuma dalilin hakan kan saka iyayen mijin tsanar matan ‘ya’yansu ta yadda za su zamo tamkar kishiyoyinsu, har ta kai ga sirikan sun zama abokan gaba.
Ko me ya ke saka su aikata hakan?, wanne irin matsaloli hakan ke iya haifarwa?, ko ta wacce hanya za a yi kokarin ganar da sirikai masu irin wannan halin?. Dalilin hakan shafin Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa, inda suka bayyana nasu ra’ayoyin kamar haka:
Sunana Abubakar Muhammad Shehu daga Jihar Kano:
Gaskiya hakan ba daidai bane saboda, abin da ya ke yi haki ne a kansa ya zama dole. Abin da ya ke sa su haka, son zuciya ne kuma babu fahimta a tsakanin su. Matsalar da ya ke haifar wa ita ce zai sa ita matar ta daina ganin girman sirikar ta su hakan na iya raba ‘ya’yan da matan, idan ni ne zan yi kokari mu fahimci juna tsakanina da ita kamar janyo mata aya da hadisai da dai sauransu. Shawara ta a nan ita ce ya kamata tayi kokari ta hada kan iyalanta domin hakan raba kan iyalanta ne da jikokinta, ina godiya ina yi muku fatan Alheri.
Sunana mustapha Abdullah Abubakar (daga garin Jos):
Yana daya daga cikin abubuwa mafi girma wajan mutuwar Aure ko da kuwa akwai soyayya mai karfi tsakanin ma’aurata, uwar miji ba ta da wata alaka da abun da danta ya ke siyowa matar sa. Ko da addinin musulunci bai ce dole idan maigida zai yi wa matar sa wata hidima ta rayuwa sai ya fadawa mahaifiyar sa ba. Mafi yawancin irin wannan sirika ko (uwar miji) son zuciya ne kawai domin cimman wata bukatar su ta Rayuwa. Gaskiya akwai matsaloli da dama kamar rashin ganin girman juna, da kuma rabuwar aure duk dalilin sirika masu aikata irin wanna halin. Matakin da zan dauka shi ne; zan kai kukana ga Allah subhanahu wata’ala domin na san shi ne zai biya mun dukkan bukatu na, daga bisani zan yi kokarin kai karar ta wajan malaimai domin tunatar da ita hakkoiki na a wajan mijina, da kuma ita ma nata hakkin a gun mijina. Shawara ta shi ne yana da kyau sirikai (iyayen miji) su rike girmansu, a matsayinsu na manya, kuma abun kwaikwayo ga zamantakewar Aure.
Sunana Habiba Mustapha Abdullahi daga Jihar Kano:
Shawarata anan shi ne gaskiya ire-iren wannan abun ya kan kawo ci baya ga rayuwar ‘ya’yansu, dan Allah kowa ya tsaya a iya matsayisa, muguwar shawara ta kawaye iyayyen miji da yawan zuwa gidan yara, rashin zaman lafiya da mugaye kalamai ka ji ana cewa Allah ya sa ta mutu mu huta da dai soransu, yawan hakuri da rashin maida magana da yawan ambaton Allah, dan allah sirrikai mu ke yawan bawa zuciyar mu hakuri saboda kowa yana da mace kuma idan an yi wa ‘yar ki ba za ki ji dadin haka ba, da Allah mu kula sosai.
Sunana Masa’ud Saleh Dokadawa:
To a gaskiya haka yana faruwa, surukai mata suna sawa matan ‘ya’yansu ido kan duk wata kyautatawa da suke yi masu, da yunkurin hana mazajen yi wa matan abubuwan jindadi. Ba daidai bane kuma su ma sun haifi ‘ya’ya matan, idan aka yi musu ba za su ji dadi ba. Abin da ya sa suke aikata hakan sun hada da; Rashin samun kyautatawa daga ‘ya’yan nasu mazan, Ganin kyashi akan abin da mazan ke wa matansu, Rashin ganin girman surukan da karancin yi musu biyayya, yana sawa suruka ta takurawa matar da, Karancin tausayi da ganin kyashi daga iyayen mijin, Karancin tsoron Allah da ilimin addini. Rashin zaman lafiya a cikin zuria, yawan samun mace-macen aure don iyayen mijin na saka ‘ya’yansu su saki matan ko da ba sa so, yana kawo raini, wulakanci, gaba tsakaninmu ko danginsu duka biyun. Idan ni ce zan yi iya kokarina wajen yi mata biyayya sau da kafa, don samun farin cikin mijina, sannan zan dinga yawan kyautata mata tsakanina da Allah, akwai hadisin Annabi Muhammad (S.A.W) yana cewa “an lullube zukata da son wanda ya kyautata mata, da kin wanda ya munana mata”. Sai kuma yawaita addu’a dare da rana akan Allah ya ganar da ita ta daina, sai nasihohi kadan-kadan. Su ji tsoron Allah su daina don hakan rashin tausayi ne da zalinci, kuma hali ne mara kyau, wanda bai dace da iyaye ba ta ko Ina.
Sunana Fatima Jaafar Abbas daga Rimin Gado LGA:
Gaskiya dai iyayen miji masu saka ido ko kuma su dinga kishi akan abin da miji ya ke wa matarsa hakan ba daidai bane, domin ita dole ce a gare shi ya kiyaye duk wasu hakkokinta kamar yadda Musulunci ya tanada ita kuma mahaifiya ya kyautata mata daidai da shari’a ita ma, don haka kuskure ne sirikai ke yi akan haka. Gaskiya son zuciya ne ya ke sa su suyi haka kuma su in sun kai ‘ya’yansu mata wani gidan za su so a kyautata musu. Hakan na janyo manyan matsaloli daga ciki yana sa har ayi (SAKI) yana kuma janyo raini ita yarinyar ta raina uwar mijin daga nan kuma sai matsaloli su yi ta yawa. Idan ni ce matakin da zan dauka shi ne; zan yi hakura a mataki na farko in yi Mata uziri in kuma dinga kyautata mata ta wannan hanyar ne zan samu in janyo hankalinta don ta daina. Iyayen mijin su ji tsoron Allah ita ma matar ta dinga kyautata wa mahaifiyar mijinta don ita ma mahaifiyar ta ce.
Sunana Zulkifilu Lawal (NAKA SAI NAKA):
Uwar miji wadda take sa ido akan abin da danta ya ke yi wa matarsa gaskiya bai kamata ba, ya kamata uwar miji ta sani ita ma matar tana da iyaye kuma tana sonsu, amman soyayyar da take yi wa danta ya sa ta zabi zama da shi, ta rabu da nata iyayen. Bai kamata uwar miji tana kishi da matar danta ba saboda wata hidima daya ke yi mata ba, yin hakan ya kan iya haifar da raini a tsakaninsu, mataki shi ne sai an kara hakuri da juriya da kai zuciya nesa da karantar halayen surikan, ya kamata surikai su sani matan ‘ya’yansu ba kishiyoyinsu bane, Allah ya sa mu dace.
Sunana Fadila Lamido daga Jihar Kaduna:
Allah ya shiryeta ta daina saka idon, domin ita ya kamata ta dinga daura danta a hanya, tana nuna mishi yadda zai kula da matarshi. Matar danki ai ba kishiyarki ba ce, abin da ya ke kawo hakan a tunanina son zuciya ne zai sa ta kasa daukar matar yaron a matsayin ‘yarta, in da ta dauketa ‘yarta kamar yadda mijin ya ke danta ba za ta yi kishi da ita ba, domin ta san matsayinta ya zarce na mata, ita uwa ce gaba daya. Kuma in da ace tana da yariya mace ba za ta so uwar mijinta ta sa mata ido ba, saboda wannan ‘yar ta ce ta san ciwonta. Matsalar da hakan ya ke jawowa na farko raini zai shiga tsakaninki da matar danki, domin duk ranar da ta fahimci kishi kike da ita za ta raina ki, daga baya kuma kiyayyarki za ta shiga zuciyarta, ke kina jin haushinta ita ma, tanajin haushinki, dan za ta dinga ganin kin takura mata, matsayinki daban, nata daban. Kuma a matsayin ki na uwa ya dace tun kafin danki yayi aure ki tarbiyantar da shi kulawa da ke, ya zamar masa jiki ta yadda idan yayi aure sai dai ki dinga kara karfafa mishi guiwa wajen sauke nauyin dake kanshi. Idan ni ce na samu uwar miji irin wannan, matakin da zan dauka shi ne; ba zan dinga bari ta san motsina ba, zan ja hankalin mijina ya suturta siyayyata, ya bayyana nata, tare da yi mata hidima a bayyane, hakan zai sa ta ji ta gamsu ta bar mu mu zauna lafiya, domin wani lokacin mai hali baya canza halinshi.