Sabon shugaban karamar Hukumar Bebeji dake Jihar Kano Alhaji Ali Namadi ya rasu kwana daya da zabarsa a matsayin shugaban karamar ta Bebeji a zaben da aka gudanar ranar Asabar data gaba 16 ga watan Janairun shekara ta 2021. Daraktan yakin neman zabensa Ibrahim Adamu Tiga ne ya tabbatar da faruwar al’amarin ga manema labarai a Kano da safiyar Talatar nan.
Marigayi shugaban karamar Hukumar ta Bebeji an zabe shi a matsayin shugaban karamar Hukumar karkashin tutar Jam’iyyar APC a zaben kananan hukumomin da ya gudana ranar Asabar.
A cewar sa, Alhaji Ali Namadi na cikin koshin lafiya a ranar litinin har sai da ya karbi baki zuwa karfe 10:30 na dare duk da cewa yana da matsalar hawan jini. Ibrahim Adamu Tiga ya ci gaba da cewa da misalin karfe 12:30a.m, ranar talatar jinin sabon shugaban karamar Hukumar ya hau, wanda hakan ta sa aka gaggauta tafiya dashi babban asibitin garin Bebeji inda kuma anan ya rasu minti goma da isarsu asibiti ya ce, za a gudanar da Jana’izarsa da misalin karfe 10:00 na safiyar Talata a garin Bebebji.