Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, yana hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) kan zargin karkatar da kudaden gwamnati.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an EFCC na yi masa tambayoyi kan zargin da ake yi masa na aikata almundahana.
- Yara 160,000 Ne Ke Dauke Da Cutar HIV A Nijeriya – NACA
- Gwamnatin Kebbi Ta Dakile Yunkurin Lakurawa Na Satar Shanu
Wasu rahotanni sun ce an kama shi ne, yayin da wasu ke cewa ya je ofishin EFCC da kansa tare da lauyoyinsa.
Wannan lamari ya biyo bayan zaman kotu da aka yi a ranar 14 ga watan Nuwamba, inda EFCC ta nemi a dage sabuwar karar da ta shigar kan Bello zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba.
Hukumar ta bayyana cewa wa’adin kwana 30 na sammaci da aka bayar bai kare ba.
A yayin da bincike ke gudana, ana sa ran samun karin bayani daga baya.