Gwamnatin Jihar Legas ta ce an shirya wata ganawa da kungiyar jin dadin direbobi ta kasa JDWAN a kan yajin aikin da direbobi ke ci gaba da yi a ranar Laraba.
Direbobin dai sun fara yajin aikin na kwanaki bakwai ne a ranar Litinin, bisa zarginsu da karbar kudaden da ake zargin hukumomin kula da wuraren shakatawa da gareji a jihar.
- Xi Ya Jaddada Sake Farfado Da Yankunan Karkara Yayin Da Ya Ziyarci Shaanxi Da Henan
- Dubun Wanda Ya Kashe Mahaifinsa Ta Cika A Legas
Wannan lamari ya sa matafiya da dama a jihar shiga damuwa a ranar Litinin, yayin da aka samu karin farashin kaya daga wajen masu ababen hawa.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin Legas ta fitar, ta ce an gudanar da wani taro da kungiyar a ranar 28 ga watan Oktoba, inda aka sake yin wani taron a ranar Laraba.
A cewar sanarwar, mai ba gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin sufuri, Sola Giwa, ya kara da cewa gwamnatin Legas na duba bukatun direbobin “da nufin samar da mafita ta din-din-din kan batutuwan da kungiyar ta gabatar.
“Ya bayyana cewa a ci gaba da sanarwar da JDWAN ta bayar na shiga yajin aikin kwanaki bakwai daga ranar 31 ga watan Oktoba, 2022, gwamnatin jihar ta hannun ma’aikatar sufuri ta gayyaci shugabanninta zuwa wani taro a ranar Juma’a 28 ga Oktoba, 2022, duk da rashin alakarta da wata kungiyar sufuri, irin su NURTW da RTEAN, da jihar ta sani,” in ji sanarwar.
“A cewarsa, yawancin ’yan kungiyar da suka halarci taron sun fito ne daga bangaren Badagry kuma an yanke shawarar dage taron har zuwa ranar Laraba 2 ga watan Nuwamba, 2022 don an hada da wakilan sauran kungiyoyin da aka amince da su tare da kungiyar duba da warware lamarin cikin ruwan sanyi.“
Yayin da ya ke bayyana sakamakon taron karo na biyu da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba ga jama’a, Giwa ya bukaci ‘yan kungiyar ta JDWAN da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da fargabar zagi da ko tsangwama ba domin an umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da doka da oda.
Mashawarcin na musamman ya kuma gargadi wadanda ke cin gajiyar yajin aikin m “da su daina yin hakan ko kuma su fuskanci fushin hukuma.