Malaman jami’o’i a karkashin kungiyarsu ta ASUU sun ratse daga shiga yajin aiki, bayan gwamnatin tarayya ta gayyace su wani taron gaggawa bisa barazanar da suka yi.
Wannan taron gaggawar ya gudana ne karkashin Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, wanda ya gudana a ranar Talata 6 ga watan Afrilun shekarar 2021 da misalign karfe 11 na safe, a shalkwatan ma’aikatar ilimi ta tarayya da ke Abuja.
A cikin wata sanarwar da jami’in hudda da jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya, Mista Ben Bem Goong ya fitar a ranar a Abuja, ya bayyana cewa ministan ilimi ya kira taron na gaggawa ne da nufin dakatar da barazanar da malaman suka yi ta cewa matukar gwamnati ba ta cika alkawuran da ke tsakaninsu ba za su kaurace wa jami’o’i.
Idan za a iya tunawa dai, kungiyar ASUU ta fitar da sanarwa da ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta ki amincewa da wasu yarjejeniyar da suka cimma a tsakaninsu. Kungiyar ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta tsanduma na tsawon watanni 10 a watan Janairun wannan shekarar bayan cimma yarjejeniya da gwamnati.
An bayyana cewa, an cimma yarjejeniya tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya kafin dakatar da yajin aikin. Wasu malaman jami’o’i ba a biya su albashi ba tun a watan Fabrairun shekarar 2020, yayin da wasu daga ciki aka biya su a cikin wannan shekarar da muke ciki.
Wani malamin jami’a wanda ya bayyana cewa ba shi ne mai magana da yawun bakin ASUU ba, ya bayyana wa manema labarai cewa, duk wani dan kungiyar ASUU da ya ki bin tsarin IPPIS wanda gwamnatin tarayya ta bukaci a yi, to ba a biya su albashi ba tun daga watan Janairu har zuwa yau.
Ya kara da cewa, mafi yawancin malaman jami’o’in da suka yi tsarin IPPIS suna amsar albashinsu har zuwa yau, wanna yana daya daga cikin yarjejeniyar da kungiyar ta cimma da gwamnatin tarayya.
Ya ci gaba da cewa, wannan yana daya daga cikin abubuwan da ya sa kungiyar ASUU ta fusata wacce ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya tana ikirarin babu kudaden da za ta cika wa kungiyar ASUU alkawarin da ta yi mata a baya.
“Kamar yadda nake magana da ku a halin yanzu, wasu malaman jami’o’in ba su sami komi ba daga cikin albashinsu tun watan Fabarairun wannan wata har zuwa wannan lokaci. Haka kuma, wadanda suka ki yin tsarin IPPIS ba su sami albashinsu ba tun daga watan Janairun har zuwa yau.
“Ina tunanin shugabannin kungiyar ASUU sun yi hakuri, saboda yadda gwamnati take ikirarin babu kudi a ko’ina da za ta yi amfani da su wajen cimma bukatun kungiyar, tabbas mu malaman jami’o’i za mu ji zafi, amma daliban jami’o’i ne za su fi jin zafi daga karshen wannan lamari.
“An dakatar da yajin aikin da kungiyar da tsunduma a baya da niyyar cewa gwamnatin tarayya za ta cika yarjejeniyar da ta yi a baya da kungiyar, amma sai muka fahimci cewa wannan farfaganda ne da yaudarar mutane. Akwai mutanan da suke yin wannan abu da ganga shi ya sa lamarin yake faruwa a haka,” in ji shi.
Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Ayo Akinwole ya zargi gwamnatin tarayya da kasa cika yarjejeniyar da ta yi da kungiyar malaman jami’o’i. Haka kuma ya yi gargadi da cewa, idan aka kasa cika wannan yarjejeniya, to zai shafi rashin ci gaban ilimi a nan gaba. Akinwole ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta biya albashin malaman jami’o’in ne na wata biyar kacal, yayin da sama da malaman jami’o’i 100 ba a biya su albashi ba a tsakanin wata uku zuwa wata 10.
Ya ce, “an dakatar da yajin aiki da aka shiga ne bisa yarjejeniyar da kungiyar ASUU ta cimma da gwamnatin tarayya a taron da ya gudana a ranar 22 ga watan Disambar shekarar 2020.
“Dukkan bangarorin guda biyu tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kungiyar ASUU sun amince babu wanda zai karya alkawarin yarjejeniyar ta hanyar sauke nauyin da ya rataya a wuyarsa.”
A cewarsa, lokacin da kungiyar ASUU ta amince za ta koma ta ci gaba da gudanar da aikin da ya wajaba a kanta, ya kamata a ce gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta dauka a bangaren ta.
…Yajin Aikin Malaman Kwalejojin Fasaha
Kungiyar malaman kwalejojin kimiyya da fasaha (ASUP) ta ayyana shiga cikin yakin aikin sai baba ta gani, sakamakon karancin kudade. Kungiyar ta bayyana hakan ne bayan da gwamnatin tarayya ta kasa shawo kan matsalolin da kwalejojin kimiyya da fasaha suke fuskanta wanda ta yi alkawarin magancewa tun a watanb Maris ta shekarar 2020.
Wannan mataki ya zo ne kasa da mako daya da likitoci karkashin laiman kungiyar likitocin Nijeriya (NARD) ta tsunduma cikin yajin aiki a dukkan fadin kasar nan sakamakon rashin biyan su alawus da sauran abubuwa.
Kungiyar ta dauki wannan mataki ne lokacin da ta kira taron manema labarai a ranar Talata a garin Abuja. Shugaban kungiyar ASUP, Anderson Ezeibe ya bayyana cewa, kungiyarsa ta rufe ayyukan gaba daya kwalejojin kimiyya da fasaha da ke cikin kasar nan daga karfe 12 na ranar 6 ga watan Afrilun shekarar 2021. Ezeibe ya kara da cewa, matakin takatar da aikinsu dai ya zo ne bayan gudanar da taron kungiyar karo na 99, wanda ya gudana a Jihar Katsina cikin dare. A cewarsa, kungiyar ta tattauna da ministan ilimi da na gwadugo da wasu gwamnoni a kan lamarin, amma har zuwa yanzu babu wani yunkuri da aka yi a kan lamarin.
Ezeibe ya lissafa irin laifukan da aka yi wa malaman wadanda suka hada da rashin aiwatar da rahotan NEED na shekarar 2014 da rashin bai wa bangaran kudaden da suka dace duk da alkawarin da aka yi musu za a yi hakan tun a shekarar 2017. Ya ci gaba da lissafawa kamar haka, ci gaba da yaudaran jami’an kungiyar da rashin aiwatar da cike tazara a cikin bangaran da rashin zantar da tsarin da aka amince da shi na shekarar 65 na ritaya wanda wasu gwamnoni ba su aiwatar da hakan ba da ikirarin tsarin rashin biyan haraji da kuma gudanar da tsarin IPPIS. Haka kuma ya bayyana cewa, akwai rashin biyan bashin albashi na karin girma da rashin sake fasalin yanayin tsarin wajen aiki, wadannan abubuwa suna daga cikin abin da ya fusta kungiyar ASUP har ta dauki wannan matakin shiga yajin aiki na sai baba ta gani.