Abba Ibrahim Wada" />

Yakamata Aubameyang Ya Bar Arsenal, Cewar Shugaban Hukumar Kwallon Kafan Gabo

Shugaban hukumar kwallon kafar kasar Gabon, Pierre Alain Mounguengui, ya bukaci dan kwallon Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang akan ya koma wata kungiya da ke da tsarin samun nasarori domin ya ci gaba da kafa tarihi kafin yayi ritaya.

Dan wasan ya yi kan-kan-kan tare da wasu ‘yan kwallon a matsayin wadanda suka fi zura kwallaye a gasar firimiyar Ingila a kakar wasan da ta wuce, inda ya ci kwallo 22 tare da Sadio Mane da Mohammad Salah.

A kakar wasa mai zuwa ne kwangilarsa za ta kare a Arsenal sai dai har yanzu bai fara Magana da kungiyar ba domin sake sabuwar yarjejeniya amma kuma rahotanni sun bayyana cewa yana son barin kungiyar ne.

“A yanzu yana Arsenal, bai ci kowanne kofi ba kuma kowa yasan babban dan wasa ne wanda ya lashe wasanni sannan ya zura kwallaye da dama saboda haka dan wasa kamarsa yana bukatar lashe kofi in ji ,”Pierre Alain Mounguengui

Mounguengui ya kara da cewa ” Idan Pierre ya samu wata kungiya, gwamma ya kara gaba saboda na fahimci ba zai iya cin kofi ba a inda yake yanzu kuma muna fatan dan wasan kasar mu ya kafa tarihi a duniya.”

A watan da ya wuce, kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce yanason Aubameyang ya ci gaba da buga wasa a Arsenal kota hallin kaka sai dai abune mai wahala dan wasan wanda ya koma Arsenal a  watan Janairun shekara ta 2018 ya ci gaba da zama, ya koma Arsenal daga Borussia Dortmund a kan fan miliyan 56.

Exit mobile version