Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Didier Drogba, ya bukaci ragowar ‘yan
wasan da suke wasu kungiyoyin da suyi koyi dana Juventus wajen rage albashin da su ke karba,
domin tallafawa kungiyar a halin da ake ciki na Cutar Coronabirus
Mai koyarwa Maurizio Sarri da 'yan wasan Juventus sun yafe albashin wata hudu domin ceto
kungiyar daga tabarbarewar tattalin arziki sakamakon coronabirus kuma kudin da Juventus za ta
samu zai kai fam miliyan 90, kwatankwacin Dallar Amurka miliyan 80 a wata hudun da ba ta biya
albashinba.
An dakatar da dukkan wasanni a Italiya zuwa uku ga watan Afirilu, don gudun yada cutar
wadda ahalin yanzu sama da mutum dubu goma suka rasa ransu a kasar duka a sakamakon
cutar wadda ta samo asali daga kasar Sin wato China.
Fitattun 'yan wasan Jubentus da suka hada da dan wasan gaban kasar Portugal, Cristiano
Ronaldo da Aaron Ramsey da dai sauransu, ba za su karbi albashin watan Maris da Afirilu da
Mayu da kuma na Yuni ba.
Kafin a tsayar da gasar Serie A ta Italiya, Juventus ce ke kan gaba a teburi da tazarar maki daya
tsakaninta da Lazio sai dai a wata hira da akayi da ministan wasannin kasar, ya bayyana cewa
wataki;a ba za’a sake buga kwallo ba a wannan kakar ta bana.
Juventus ta gode wa masu horas da kwallon kafa da 'yan wasa kan wannan kokarin da suka yi a
lokacin da ake mawuyacin hali kuma ta bayyana cewa a shirye take data taimakawa gwamnatin
kasar domin yaki da cutar.