Yaki Da Boko Haram: Buhari Ya Yi Ganawar Sirri Da Sabon Shugaban Kasar Chadi

Daga Bello Hamza,

A jiya Juma’a ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da shugaban kasar Chadi Janar Mahamat Idriss Deby, ta tawagarsa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kamfanin dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ta bayyana cewa, Deby, ya dare karagar mulkin kasar ne bayan da mahaifinsa ya mutu a ranar 19, ga watan Afrilu 2021, kwana daya bayan ziyara da ya kawo Nijeriya.

An kawo ziyarar ne don ya gana tare da sanin juna da Shugaba Buhari a matsayinsa na mai fada aji a cikin shugabanin kasasshen Yankin Afrika ta Yamma da kuma Afrika gaba daya.

Shugabanin biyu sun kuma yi amfani da damar wajen tattauana yadda za su bullo wa matsalar tsaron da ya ke fuskantar yankin gaba daya. Nijeriya da kasar Chad na iyaka da juna a yankin Sahel.

Exit mobile version