Yaki Da Kansa: Bagudu Ya Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Kan Sanya FMC Birinin Kebbi

Daga Umar Faruk,

Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, a jiya ya yaba wa Gwamnatin Tarayya saboda sanya Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Kalgo a cikin Shirin Hadin gwiwar yakar Cutar Kansa a tsakanin gwamnatin Tarayya da kuma wasu jahohin kasar nan.

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya yi wannan yabon ne a lokacin da Ministan Kiwon Lafiya, Farfesa Osagie Ehanire, wanda Dakta Uche Nwokwu, mai ba da shawara kan harkokin cutar kanjamau, na Hukumar Kula da Cutar Kansa ta kasa, a Tarayyar Abuja, tare da rakiyar Paulette Ibeke, wanda ke jagorantar yakin kawar da cutar kansa, Clinton Health Access Initiatibe ta wakilta. Ya yin ziyarar Gwamna Bagudu a ofishinsa da ke fadar Gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi.

Gwamnan na Jihar Kebbi ya ce, wannan abin da Gwamnatin Tarayya ta shirin ta a karkashin jagorancin Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, zai karfafa yaki da yaduwar cutar Kansa a jahohin kasar Nijeriya baki daya.

Bagudu ya yarda da irin namijin kokarin da matar sa, Dr Zainab Shinkafi Bagudu ta yi, wurin bada gudunmuwarta yaki da Cutar Kansa a jihar kebbi da kuma wasu jahohin kasar.

Haka zalika yana mai cewa, “ta kasance mai matukar tursasawa ta hanyar yiwa Mata awon Cutar Kansa da kuma basu magugunna a kyauta kai har da shirya gangamin yekuwa na wayar da kan jama’a kan illolin da ke tattare ga Cutar Kansa musamman ga Mata. Bisa ga irin kokarin da gudunmuwarta na yaki da Cutar yana samun nasara kwarai da gaske.

“A cikin ‘yan shekarun da suka gabata. Jihar Kebbi ta taka rawar gani wajen fito wa da hanyoyin wayar da kan jama’a game da illolin cutar kansa.

“Haka nan kuma an samar da allurar rigakafin cutar kansa ga al’ummar jihar, gudanar da gwaji da dubawa da kuma ba da magani a kyauta. Dukkan rokarin da jihar kebbi ta yi ya yi kyau saboda kyakkyawan jagoranci da Dakta Zainab ta bayar kan yaki da Cutar ta kansa.

“Hakika ta kasance mai kwazo sosai a fannin yaki da cutar kansa, a cikin gida Nijeriya da kuma wasu kasashen Duniya. Dakta Zainab Shinkafi Bagudu ta taba tara matan gwamnonin wasu jahohin kasar nan don gudanar da zagayen cikin garin Birnin-Kebbi a kafa don kone Cutar Kansa mai taken” walk away Kansa.

“Wadannan tarurrukan na wayar da kan jama’a game da cutar kansa sun samu karbuwa ne daga abokan aikinta daga sassan daban-daban a cikin kasar Najeriya, tare da nuna matukar kulawa.”

Gwamnan ya kuma ce, wasu daga cikin abubuwan da ake wallafawa don fadakar wa game da yaki da kuma daukar mataki kan kamuwa da cutar kansa sun ragu sosai, Saboda irin shugabancin da Dakta Zainab tayi da kuma kulla hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki da kwararrun Likitoci kan Cutar Kansa a ciki da wajen jihar, da kuma kasar.

Har ilayau Gwamna Bagudu ya kara da cewa, ana shirin aiwatar da shirin shawo kan matsalar cutar kansa a jihar, yayin da a kayi hadin gwiwa tare da Kungiyoyin masu rajin yaki da Cutar Kansa na cikin gida da na kasa da kasa za a gudana.

A cewarsa, wannan hadin gwiwa zai maida hankali ne kan bincike, bada horo da horassuwa ga ma’aikatan kiwon lafiya da kuma na jinya da ugozuma na cikin manyaan asibitocin jihar ta kebbi don sanin makamar aikin jinyar marasa lafiya mai dauke da Cutar Kansa da kuma irin matakan kariya ga kamuwa da Cutar.

Da yake jawabinsa tun daga farko, Ministan kiwon Lafiya na kasa, mista Ehanire ya bayyana cewa, Shirin yaki da Cutar Kansa wani shiri ne na Ma’aikatar kiwon Lafiya ta Tarayya, tare da hadin gwiwar Clinton ta American Kansa Society.

Ya kara da cewa, an fito da shi ne domin rage wa masu dauke da Cutar Kansa yawan kashin kudin magani zuwa kasa da kashi hamsin cikin dari na kudaden magani.

Wakilin ministan Ya ce, Ministan ya kirkiro shirin ne a shekarar 2017, tare da cibiyoyin gwaji guda bakwai, bisa ga nasarorin da aka samu har zuwa yanzu, ya sa aka yanke shawarar fadada Shirin har zuwa irin Jihar Kebbi.

Saboda haka Minista Ehanire ya kara bayyana cewa, Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da Birnin Kebbi da Cibiyar Kiwon Lafiya mallakar gwamnatin jihar kebbi da ke a Kalgo su ne na farko kuma su kadai zasu ci gajiyar wannan fadada shirin da aka yi a duk fadin kasar.

“Wannan ci gaba ne ga irin ci gaban da gwamnatin Bagudu ta samu a fannin kiwon lafiya da sauran bangarorin da suka shafi hakan.

Ministan ya bayyana cewa “wannan ziyarar tana daga cikin ayyukan da zamu gudanar a jihar ta kebbi domin tantance kayayyakin aiki a wadannan asibitocin da aka sanya cikin shirin na yaki da Cutar Kansa a kasar Nijeriya baki daya.”

Tun da farko, Kwamishinan kiwon Lafiya na jihar kebbi , Alhaji Jafar Muhammad ya shaida wa gwamnan cewa wakilin Ministan ya zo jihar ne don tantance kayan da ke cikin asibitocin da wurin da za a fara ganin marasa lafiya masu dauke da Cutar Kansa a jihar Kebbi domin jihar ta shiga cikin shirin yaki da cutar kansa da gwamnatin tarayya ta bulo da shi.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Shugaban Ma’aikatan, Gidan Gwamnati, Alhaji Suleiman Muhammad Argungu (Jarman Kabi) Sakataren gwamnatin jihar kebbi, Babale Umar Yauri, Kwamishinan Lafiya, Alhaji Jafar Muhammad, Dakta Aliyu Abdulrahman, Dakta Jamilu , Manyan Daraktocin ma’aikatar kiwon lafiya na jihar kebbi na Federal Medical Center Birinin Kebbi da Kebbi Medical Center Kalgo da sauransu.

Exit mobile version