Bello Hamza" />

Yaki Da Ta’adanci: An Horar Da ‘Yan Kato Da Gora 441 A Jos

Mutane 441 da suka samu horo a kan yaki da ta’adanci suka karbi takardar shaidar kammala horon da aka yi musu a karshen makon daya gabata, kungiyar United Nations Debelopment

Programme  ta dauki nauyin shirya taron na daya dauki tsawon mako biyu ana yi.

An zabo maharta taron ne daga kungiyoyi ‘yan Kato da Gora da yan sintiri daga jihohin Adamawa da Borno da kuma jihar Yobe.

An gudanar da shirin ne ta hannun kungiyar  UNDP tare da hadin hannun gwamnatin kasar  Japan da Switzerland da Canada da kuma Birtaniya da kuma gudummawa daga jihohi 3 da suka anfana da shirin.

Shugaban hukumar UNDP na kasa Mista Samuel Bwalya wanda Mista

Mathew Alao Ya wakilta, a yayin bikin rufe taron da aka gudanar a dakin taro na “Citizenship

and Leadership Training Centre, CLTC” a Jos, ya ce, an shirya horas wa ne domin kara shigar da tsaffin yan Kato da Gora da yan Sintiri da kuma mayakan Boko Haram cikin alumma, ya kuma ce, za a ci gaba da shirin har sai an kakkabar da yan Boko Haram daga fadin tarayyar kasar nan tare da karkabar da dukkan sharrin da harkar taaddancin ya zo dasu.

Ya ce “Kashin farko Na shirin zai samar da karfafa yan Kato da Goran ne da kuma yan sintiri da dabarun bayar da taimako ga alummuns. Taimakon ya hada da karewa da tabbatar da kare hakkin dan Adam da bayar da kariya ga cin zarafin mata da kuma tabbatar da zama lafiya tsakaninsu”

“kashi na biyu na shirin zai bai wa halarta shirin horasawar koyon sana’ar da zas tallafa wa rayuwarsu ta yadda zasu ci gaba da amfanar alummar da suka samu kansu a ciki musamman bayan da suka tuba daga ta’addanci, yayin da kashi na uku na shirin da ake gudanarwa zai samar wa masu kamala shirin horasawar da tallafin kayan aiki da tallafin kudaden da zasu gudanar da rayuwarsu da kuma sana’o’insu.

A cewarsa “Ina matukar farin cikin gani wannnan shirin horaswar baya ga bunkasa rayuwar yan kato da goran da ‘yan sintirin na yadda zasu taimaka wajen samar da tsaro da tallafi ga jama’a ya kuma taimaka musu da hanyoyi da dabarun samar da zaman lafiya a tsakanin jama’ar da suka samu kansu, muna kuma tsananin farin cikin ganin mun bayar da gudummawar ganin faruwar haka”

Ya kara da cewa, “Aiyukan kungiyar UNDP a lokuttan baya da abin da ake yi a halin yanzu yana fitar da natijoji masu mahimmanci ga wadanda suka amfana musamman mata, wanda suke jagoran aikace aikacen gida da matasa da kuma maza”

“Cikin nasarorin a kwai kara gina gidaje fiye da 300 domin tsugunar da ‘yan gudun hijira da masu dawo wa gida bayan yaki ya lafa, da kuma kara gina wuraren gudanar da rayuwar jama’a fiye da 30 wanda suka hada da makarantu da asibitoci da ofishoshin kananan hukumomi da ofishoshin ‘yan sanda, gudanar da aiyukan ya tallafawa ‘yan aalin yankin da aiyukan yi ga mutane fiye da1,300 a sansanin ‘yan gudun hijira.

“An tallafawa ‘yan kasuwa maza da mata fiye da 1,000 wajen ganin sun farfado da harkar kasuwancinsu, an kuma samar da wasu harkokin kasuwanci ga mata da matasa fiye da 258, wadanda suka shiga shirin horasawar na hukumar UNDP, sannan akwai mutum fiye da 317 da a halin yanzu sun kamala samun horo suna jiran a yi bukin basu takardar kamala karatun nasu, za kuma a tallafa musu da kayan aiki da kudaden da zasu fara gudanar da harkokin kasuwanci da sana’o’in da suka koya. Haka kuma an samar wad a makarantu 200 a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe da wutan lantarki mai aiki da hasken rana”

Ya kuma kara da cewa, “Abubuwan da muka kammala sun hada da horas da jami’an ‘yan sanda 800 a kan hanyoyin da zasu yi hurda da fararen hula da kuma samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, an kuma horasa da jagororin alumma fiye da 700 a kan hanyoyin sasanta jama’a da tabbatar da zaman lafiya a cikin kauyuka da birane, wasu mutane fiye da 38,000 sun samu horon hanyoyin gano inda aka dasa nakiya, an kuma shirya wasan kwaikwaiyo guda 26 domin fadakar da jama’a hanyoyin zaman lafiya da fahintar juna a tsakanin alumma, musamman bukatar zaman lafiya a tafkin Chadi an kuma watsa wa mutamne fiye da Miliyan 5, sai kuma gyara kananan kotuna 19 a jihohi 3 domin karfafa hanyoyin samun adalci a cikin al’umma. An samu gaggarumin nasaran nan ne saboda kokarinmu na kara gyara wuraren da aka rusa da tsugunar da jama’ar da suka tarwatse musamman wadanda suka fada cikin rikicin daya addabi yankin Arewa maso Gabas.

Exit mobile version