Talauci babbar barazana ne ga ci gaban dan Adam ganin har yanzu akalla mutane biliyan daya na cikin matsanancin talauci a duniya. Bari mu duba yadda kasar Sin ke samar da turba mai kyakkyawan fata ga samun ingantacciyar rayuwa.
Kasar Sin ta yi nasarar tsame mutane miliyan 800 daga kangin talauci tare da cimma burin rage radadin talauci bisa ajandar ci gaba mai dorewa ta Majalisar Dinkin Duniya ta 2030 tun kafin lokacin da aka tanada. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres da kansa, ya yabawa nasarar da kasar Sin ta samu a matsayin “Nasarar yaki da kangin talauci mafi girma a tarihi”.
- Minista Ya Buƙaci Sabbin Shugabannin NIPR Su Faɗakar da Jama’a Yadda Ya Dace
- An Yi Wa Shugaban Ƙasar Brazil Lula Da Silva Tiyatar Ƙwaƙwalwa
Dabarun rage talauci na kasar Sin sun kuma taimaka ga daidaita kalubalen talauci da sauran kasashen duniya ke fuskanta.
Misali, ta hanyar manufofi irin su shawarar “ziri daya da hanya daya”, kasar Sin tana aiki da kasashe masu tasowa a duk duniya wajen samar da ayyukan more rayuwa, ilimi da kiwon lafiya. Wanda hakan ya fitar da miliyoyi daga talauci.
Haka nan kasar Sin ta yi matukar tasiri ga ci gaban tattalin arzikin Nijeriya ta hanyoyi da dama, domin ita ce babbar abokiyar cinikayyar Nijeriya. Sin ta zama babbar hanyar zuba jari ta kai tsaye daga ketare (FDI) a Nijeriya, musamman a fannin ababen more rayuwa, hakar ma’adinai, da sadarwa.
Baya ga fasahar kere-kere, da fasahohin ilmi ga masana’antun Nijeriya da kamfanonin Sin suka taimaka da kasar da ita, har ila yau kasar Sin ta taimaka wajen gina hanyoyin jirgin kasa kamar na Abuja zuwa Kaduna, da Legas zuwa Ibadan. Kamfanonin kasar Sin sun kuma gina tasoshin samar wutar lantarki, da hanyoyin sadarwa, da ayyukan sabunta makamashi daban-daban a Nijeriya.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta ba da taimakon raya kasa ga kasashe sama da 160, ta yi hadin gwiwa mai inganci na tsarin “ziri daya da hanya daya” tare da kasashe sama da 150, ta kuma tallafa wa ayyukan more rayuwa sama da 1,100 da kusan dalar Amurka biliyan 20 na tallafin raya kasa.
Gudunmawar da kasar Sin ta bayar wajen yaki da kangin talauci a duniya, bai tsaya kan bayar da taimakon kudi da fasaha kadai ba domin ta kuma horar da kwararru sama da 400,000 daga kasashe da yankuna sama da 180, tare da karfafa kokarinsu na kawar da fatara.
A wurin taron kolin G20 da aka kammala kwanan nan a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya jaddada matakai takwas da kasar Sin za ta dauka na taimaka wa raya kasa da kasa musamman ga kasashe masu karamin karfi. Duk wadannan sun sa kasashe masu tasowa amincewa da kasar Sin a matsayin amintacciyar abokiyar hulda.