Daga Khalid Idris Doya,
Hukumar bunkasa shiyyar arewa maso gabas (NEDC) ta bayyana a jiya cewa mutane dubu biyu da hamsin da shida (2,056) ne za su amfana da tallafin biliyan shida (6bn) a karkashin shirin hukumar na tallafa wa jama’a kan harkokin ilimi wato (NEDC-EEF).
A sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na hukumar Abba Musa ya fitar, ya shaida cewar mutum 2,056 za su samu tallafin karatu kyauta a manyan jami’o’i a karkashin wannan kudin.
An samar da hukumar ne dai da zummar farfado da shiyyar arewa maso gabas bayan da ‘yan ta’addan Boko haram suka daidaya shiyyar.
Da ya ke bayani kan nasarorin da suka cimma kuwa, ya shaida cewar sun jima suna tallafa wa marayu da masa karfi, kana a cikin wannan kudin ma marayu da makara galihu za su amfana sosai.
“Tallafin karatun da aka ware din zai hada da daliban jami’a masu neman digiri, da masu neman digiri na biyu, da kuma masu digiri na uku, da za a tsakulo daga jihohin arewa maso gabas. Dalibai 2,056 daga gundumomi 1,028 da ke arewa maso gabas ne za su amfana da wannan tallafin.
Kan nasarorin da suka cimma tun bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da hukumar a 2019 a karkashin jagorancin Janar Pau Talfa (ritaya) da Mohammed Alkali, sun samu nasarar gudanar da ayyukan jinya kyauta ga marasa lafiya da daman gaske.
Ya ce, daga cikin marasa lafiyan da hukumar ta dauki nauyi har da tiyata da sauran muhimman fannoni da aka taimaka wa majinyata dubbai.
Ya ce, ko bayan barkewar annobar Korona hukumar ta taimaka wa gwamnatocin shiyyar da dama wajen samar musu da kayyakin kula da lafiya da rage yaduwar cutar domin dakilewa tare da kariya, inda yake mai cewa sun gudanar da muhimman ayyuka na tallafi dukka a kokarin hukumar na farfado da shiyyar arewa maso gabas.