‘Yan bindiga na ci gaba da addabar arewa maso yammacin Nijeriya, al’amarin da ke daidaita al’ummar yankin duk da jami’an tsaro na samun galaba a kansu kamar yadda rundunonin tsaro suka sha bayyanawa.
Al’ummomin kauyuka 10 da suke karamar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna sun tsere, inda suka bar gidajensu domin tsira da rayukansu sakamakon aikace-aikacen ‘yan fashin daji da suka addabi yanki.
- Abubuwa Uku Da Za A Yi Farashin Kaya Ya Sauka A Nijeriya – Dakta Saleh
- Za A Fara Amfani Da Sabon Layin Jirgin Ƙasa Na Dakon Kaya Daga Legas Zuwa Kano A Watan Gobe
An tattaro cewa wadanda lamarin ya fi shafa mata ne da yara, sun yi tattaki na tsawon zango domin neman wurin da za su yi gudun hijira a cikin babban garin Giwa.
Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Giwa ta yamma a majalisar dokokin Jihar Kaduna, Umar Auwal Bijimi ya shaida wa majiyarmu cewa tashin hankalin ya faru ne tun lokacin da aka janye jajirtaccen soja, Sajet Usman Hamisu Bagobiri, wanda ya ba da gagarumin gudummuwa wajen dakile motsin ‘yan fashin daji a yankin.
Ya ce, rashin kasancewar Sajet Bagobiri a yankin ya bai wa masu aikata laifuka kwarin guiwar ci gaba da tsula tsiyarsu, lamarin da ya janyo jama’a na neman tsira da rayukansu daga kauyuka da daman gaske.
Ya nuna damuwarsa kan garkuwa da mutane na baya-bayan nan da aka yi, musamman na mata, lamarin da ya sanya al’ummomin yankin yanke hukuncin barin gidajensu.
Bijimi ya ce, yankunan da abun ya sha sun hada da Gogi, Angwar Bako, Marge, Tunburku, Bataro, Kayawa da kuma Yuna.
Ya roki gwamnatin jihar da rundunar sojin Nijeriya da su sake dawo da Sajen Bagobiri yankin shi da sauran sojoji masu azamar taimaka wa yankin wajen ganin an kare jama’an yankin daga ‘yan fashin daji, da tabbatar da kare rayuka da dukiyar al’umma domin ganin sun koma gudanar da harkokin nomansu yadda ya kamata.
Sarkin Fatika, Nuhu Lawal Umar ya yi kira da a samar da tsaro a yankin, yana mai cewa yankin na matukar bukatar agajin gwamnati cikin gaggawa.
Kwamishinan tsaron cikin gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya ce masu ruwa da tsaki ciki har da shugaban karamar hukumar Giwa, Alhaji Abubakar Shehu Giwa, da shugabannin al’umma sun zauna domin gaggauna yadda za a kyautata lamarin tsaro a yankin.
Ya tabbatar da cewa ana kan kokarin ganin an kawo karshen matsalar tsaron yankin kuma tuni aka dauki matakan inganta samun bayanan sirri da kyautata matakan tsaro a wadannan yankunan.
Haka zalika, ‘Yan bindiga sun kashe mutane takwas tare da yin awon gaba da manajan bankin Taj, Mandir Laura a Jihar Zamfara.
LEADERSHIP ta gano cewa ‘yan bindigar da ke dauke da makamai, wadanda adadinsu ya kai kimanin 15 sun mamaye gidan manajan bankin da ke yankin
Rijiyar Gabas a daren ranar Litinin, inda suka yi awon gaba da shi.
A wani harin na daban, ‘yan bindiga sun kai hari garin Faru da ke karamar hukumar Maradun a jihar, inda suka kashe mutane takwas.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun yi wa yankin kawanya kafin su kaddamar da harin nasu.
Majiyoyin sun kuma kara da cewa an sace mutane tare da tafiya da su cikin daji.