Daga Khalid Idris Doya,
Mutum biyar ne aka bada rahoton kisan su wanda wasu ‘yan bindiga dadi suka aikata da safiyar jiya Lahadi a wasu hari daban-daban da suka faru a kananan hukumomi biyu na jihar Benuwai.
Majiyarmu ta nakalto cewa uku daga cikin wadanda aka kashen masu bindigan sun kutsa kai cikin gidan Inna Jato wani tsohon dan majalisar jihar mai wakiltar mazabar Kastina-Ala ta gabas da ke kauyen Nagu a karamar hukumar Kastina-Ala ta jihar.
Ganau sun shaida cewa an kuma lalata kadarori da dukiyar jama’a tare da banka wa gidajen jama’a wuta a harin da suka kai kauyen Kastina-Ala.
Babban sakataren watsa labaran shugaban karamar hukumar Kastina-Ala, Tertsea Benga, ya shaida cewar zan iya tabbatar da kisan mutum uku ne kawai wadanda aka kai musu hari a gidan tsohon dan majalisar.
Benga ya shaida cewar lamarin ya faru ne cikin daren ranar ta Lahadi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Catherine Anene ta tabbatar da mutuwar mutum biyar din, tana mai cewa ba su kai ga kammala tattara bayanan kisan da aka yi a Kastina-Ala ba zuwa yanzu.
Anene ta ce, mutum uku, da ya hada da wani mutum da matarsa da dansa guda ne aka kashe a Kastina-Ala, a kauyen Naka kuma wasu matasa biyu su ma sun rasa rayukansu lamarin da ya kawo adadin mutum biyar wadanda suka mutu.
Ta ce, sun kaddamar da bincike domin kokarin gano musabbabin lamarin tare da yunkurin daukan matakan da suka dace domin dakile faruwar hakan gaba.