Connect with us

LABARAI

Yan Bindiga Sun Hallaka Makiyaya 2 Da Sace Shanu 103 A Kogi.

Published

on

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne, a ranar alhamis da ta gabata sun kashe Fulani makiyaya biyu tare da awon gaba shanu dari da uku a kauyen Osuku dake yankin karamar hukumar Koton karfe a jihar Kogi.

Mai martaba Ohimegye Igu na Koton karfe, Alhaji Abdulrazak Isah Koto ne ya shaidawa wakilin jaridar LEADERSHIP A Yau LAHADI hakan a jiya asabar a garin Lokoja.

Alhaji Abdulrazak Isah Koto ya ce, ya samu kiran gaggawa daga Ardon fulanin yankin da misalin karfe 11.23 na daren ranan alhamis inda ya shaida masa cewa yan bindiga sun kai hari rugarsu. Sarkin na Koton karfe ya kara da cewa nan take ya tattaro yan sintirin wadanda suka shiga farautar yan bindigan kuma suka samu nasarar kwato wasu shanun da yan bindigan suka sace.

Ya kuma nanata bukatar dake akwai na ganin an samar da karamin barikin sojoji a babban hanyar Abuja zuwa Lokoja domin dakile yawan kai hare haren da yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane suke yi domin kare lafiya da kuma dukiyoyin jama’a.

Haka shima babban mai baiwa gwamna shawara ta musamman akan sha’anin tsaro na karamar hukumar Koton karfe, Abdulkarim Isah ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace tuni ya tura jami’an tsaro domin kwato sauran shanun da yan bindigan suka sata.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: