Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyuka takwas a jihohin Kebbi da Neja, inda suka kashe mutane 33, da yin garkuwa da mutane 30 tare da sace shanu 2,000.
A jihar Neja, ‘yan bindigar sun kashe wasu mutane a kauyuka uku tare da yin awon gaba da wasu 30 a Garin Gidigore da ke karamar hukumar Rafi a wasu kauyuka dake kan iyaka da jihar Kaduna.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Garin Gidigore yana da tazarar kilomita kadan daga Birnin-Gwari a jihar Kaduna inda ‘yan bindigar ke da sansanoni da dama a dazuzzukan.
An gano cewa ‘yan bindigar sun kai farmakin ne tun daga daren ranar Talata da misalin karfe 10:30 na dare zuwa safiyar Laraba, sun kuma kona gidaje da dama a kauyukan.
A harin da aka kai a Kebbi, wasu ‘yan bindiga sama da 200 a kan babura da sanyin safiyar Talata sun kai hari a wasu kauyuka bakwai a karamar hukumar Danko-wasagu ta jihar.
LEADERSHIP ya rahoto cewa an kashe Mutane har 30 tare da satar shanu sama da 2,000.
Wasuda dama sun samu raunuka a harin yayin da wasu suke jinya a asibitocin Wasagu da Ribah.