‘Yan fashin daji sun kashe wani mazaunin kauye wanda ya kai musu kudin fansa a Kaduna, lamarin ya jefa al’ummar kauyen Kidandan da ke karamar hukumar Giwa cikin firgici da razani.
Wanda suka kashe din, shi ne Abdullahi Haruna, mamban kungiyar agaji ta Fitiyanul Islam. Haruna ya amince kan cewa zai dauki kudin fansa ya kai musu domin ceto wani dan kauyen da masu garkuwan suka sace.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Dagaci Tare Da Sace Mutane Da Dama A Neja
- Tinubu Ya Nada Olukoyede A Matsayin Sabon Shugaban EFCC
Lamarin ya faru ne da karfe 2: pm na ranar Laraba a wani wajen da aka fi sani da Sabon Layin Kidandan.
Wani dan banga da ya nemi a sakaye sunansa ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin a ranar Alhamis.
Kazalika, shugaban matasan yankin Jamil, ya shaida cewar, ‘yan fashin dajin sun bukaci kudin fansar wani da suke tsare shi, inda shi kuma Abdullahi Haruna ya amince zai dauki kudin domin ya kai musu.
Wata majiya ta ce ‘yan bindigan sun yi kokarin tursasa Haruna ya biyo su zuwa inda suke inda suke nemi ya sauko daga kan mashin dinsa domin binsu, sai ya ki inda ya ce shi ya zo ne kawai domin ya kawo musu kudin fansa ba wai binsu ba.
Bayanai na nuni da cewa, kauyen Sabon Layi ya zama wani cibiyar amsar kudin fansa musamman na mutanen da aka yi garkuwa da su a wannan yankin.
Dukkanin kokarin jin ta bakin kakakin ‘yansandan jihar, ASP Mansir Hassan ya citura domin ba a sameshi a waya ba.