Connect with us

KASASHEN WAJE

‘Yan Bindiga Sun Kashe Dogarawan Tsaro Na Juyin Juya Hali A Iran

Published

on

Jami’ai sunce an kashe ‘yan bindigar biyu. Wasu kuma rahotanni na cewa an kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a kai harin.

Kungiyar IS da wata kungiyar larabawa ta gwagwarmayar ‘yan to Ahbaz, sun dauki alhakin harin da aka kai yankin Khuzestan.

Kafar labaran Iran, ta ce maharan sun kai harin ne wani waje da jami’an kasar suka taru domin kallon faratin da aka saba yi duk shekara, domin murnar zagayowar ranar da aka kafa jamhuriyar musulunci a tsakanin alif 980 zuwa alif 988 bayan yaki da kasar Iraki. An gudanar da makamancin wannan fareti a wasu sassan kasar.

Akasarin mutanen da suka mutu dogawan tsaro na juyin juya halin kasar Iran ne. haka kuma wasu rahotanni na cewa daga cikin wadanda suka mutu din akwai wani dan jarida.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: