An harbe wasu ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka hudu a Nijeriya har lahira a karamar hukumar Ogbaru da ke Jihar Anambra.
Majiyoyi sun shaida wa cewa, an bude wa ayarin jami’an ofishin jakadancin wuta a lokacin da suke wucewa ta yankin.
- Magana Maras Dacewa Ta Jakada Brigety Na Tare Da Wani Makasudi
- Tinubu Da Kwankwaso Sun Gana A Faransa
Wata majiya ta ce wadanda harin ya rutsa da su na gudanar da ayyukan jin kai ne a yankin yayin da wata majiya ta ce jami’an da aka kai wa harin na son hada hanyarsu ta karamar hukumar Ogbaru.
“Akalla mutane hudu ne suka mutu a harin yayin da wasu suka samu raunuka. Sojoji sun mamaye yankin a yanzu,” cewar majiyar.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu cikakken bayanin harin ba, sai dai kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin ba tare da bayar da cikakken bayani ba.
“Bayan samun labarin harbe-harbe a yankin Ogbaru, kwamishinan ‘yansanda CP Echeng Echeng ya tura tawagar ‘yansanda karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yansanda mai kula da ayyuka domin kai dauki.
“A halin da ake ciki, babu cikakken bayanai game da lamarin har yanzu suna kan aiki, zan yi cikakken bayani daga baya.”
Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya kuma tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’anta na hada kai da jami’an tsaron Nijeriya domin sanin tushen lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp