Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane 15 a wani hari da suka kai a wani masallaci da ke Unguwan Mantau, ƙaramar hukumar Malumfashi a Jihar Katsina.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Abubakar Sadik Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
- NNPP Za Ta Iya Goyon Bayan Takarar Tinubu A 2027 – Sakataren Jam’iyyar
- An Gano Karin Gawarwaki 3 Da Jirgin Ruwa Ya Kife Da Fasinjoji 26 A Sokoto
Ya ce harin ya auku ne lokacin da mutane ke tsaka da yin sallar Asuba.
DSP Aliyu ya bayyana cewa, harin ramuwar gayya ne kan mazauna unguwar, bayan da suka yi ƙoƙarin kare kansu daga farmakin ‘yan bindiga a kwanakin baya.
A halin yanzu, gwamnatin jihar ta ɗauki matakan tsaro don kwantar da tarzoma a yankin.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, ya ce jami’an tsaro sun shiga Unguwan Mantau domin tabbatar da zaman lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp