‘Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da sace wasu mutane 130 a kauyen Goran Namaye da ke karamar hukumar Maradun a Jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin mai suna Salisu Lawali, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa ‘yan bindigar sun yi wa garin kawanya ne da misalin karfe 1:00 na daren ranar Alhamis.
- Shari’ar Ganduje Ta Ɗauki Zafi, An Sauya Alƙali
- JAMB Ta Sake Fitar Da Wasu Sakamakon Jarrabawa 36,540
Lawali ya kara da cewa wadanda aka yi garkuwa da su galibi mata ne da kuma wasu maza, inda ya tabbatar da kashe mutane uku a yayin harin.
“Yayin da nake magana da ku, da yawa daga cikin mutanenmu sun bace kuma an kashe mana mutane uku a wannan mummunan lamari,” in ji shi.
Mazaunin garin ya kuma kara da cewa ‘yan bindigar sun zo da yawa a kan babura dauke da muggan makamai.
Ya kara da cewa “Sun zo da yawa kuma sun mamaye kauyen gaba daya, inda suka sace mutane da dama.”
Lawali ya yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su kawo musu dauki.
“Ina so na yi kira ga gwamnatin tarayya da na Jihar Zamfara da su turo mana jami’an tsaro domin gano maboyar wadannan ‘yan ta’adda da kuma kubutar da mutanenmu.”
Ya zuwa yanzu babu wata sanarwa daga jami’an tsaro a jihar kan faruwar lamarin.