Connect with us

LABARAI

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 11 A Filato

Published

on

‘Yan bindiga sun kashe mutum 11 a kauyen Lopandet Dwei dake a masarautar Du ta karamar hukumar Jos South dake cikin jihar Filato, kamar yadda rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar a ranar Litinin.
Jami’in watsa labarai na rundunar ‘yan sandan, DSP Terna Tyopeb, ya bayyana wa anfanin Dillancin labarai ta NAN ce a kai harin ne ranar Lahadi da daddare.
“Jiya da misakin karfe 8:30. na dare a ka kira mu ana bayanin cewa, ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Lopandet Dwei Du dake karamar hukumar Jos South ta jihar.
“Nan take muka nufi inda abin ya faro amma kafin mu kai wurin maharani sun tsere kuma har sun harbi wasu mutane.
“Daga nan ne muka wuce da wadnda abin ya rutsa das u zuwa asibitin koyarwa ta jami’ar jos (JUTH) da kuma asibitin kwararru da garin Jos.
“Likitoci a dukkan asibitin sun tabbatra da mutuwar mutum 11 yayin da mutum 12 kuma suka ji munanan raunuka ana kuma ci gaba da basu magani,” inji shi.
Mista Tyopeb ya kuma kara da cewa, an tura jami’an tsaro dauke da makamai don tabbatar da doka da oda da kuma kare aukuwar rikicin.
Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu a na ci gaba da kokarin an cafke kadanda suka kai harin da nufin hkunta su.
Jami’in watsa labaran ‘yansanda ya kuma bukaci mutane yankin su kwatar da hankalinsu su kuma bi doka da oda, don kuwa ‘yan sanda na ci gaba aikin ganin sun kare dukiya da rayukan jama’a gaba daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: