‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 60 A Kauyukan Zamfara

A wani sabon rahoto daga Jihar Zamfara mai fama da hare-haren ‘yan bindiga, na tabbatar da ‘yan ta’addan sun kashe akalla mutum 60 a wasu kauyuka a fadin jihar Zamfara. Kurfa Danya, Kurfa Magaji Rafin Gero, Tungar Isa da Barayar Zaki dake kananan hukumomin Bukkuyum da Anka a jihar.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun zo ne a kan babura, inda suka dinga budewa mutane wuta ba kakkautawa, sannan suka cinna wa rumfuna da gidaje wuta; inda yara da mata suka dinga gudun neman tsira. Wadanda suka tsira daga hare-haren suna gudun hijira a Karamar Hukumar Bukkuyam, da dama daga cikinsu sun dauke da raunukan harbin bindiga a jikinsu.

Har lokacin hada wannan rahoton ba a san mutum nawa bane suka bace, sannan gawarwakin wadanda aka kashe har yanzu suna nan ba a yi musu jana’iza ba, amma an tattara su a waje daya, saboda mutanen garin suna tsoron yi musu jana’iza; duba da cewa a wasu garuruwa da ‘yan bindigar suka yi irin wadannan hare-haren suna afkawa wadanda suke yi wa mutanen da aka kashe jana’iza.

Exit mobile version