‘Yan bindiga sun kashe sojoji biyar da wasu ‘yan kasuwa daga Ƙauyen Lilo a Ƙaramar Hukumar Mada, Gusau, a Jihar Zamfara.
Al’ummar Lilo sun yi zaman makokin rasuwar sojojin, waɗanda suka rasa rayukansu yayin artabu da ‘yan bindiga.
- Tayar Da Yaki A Zamanin Nan Kauyanci Ne
- Gwamnatin Kaduna Ta Umarci Makarantu Masu Zaman Kansu Da Su Nemi Amincewarta Kafin Ƙara Kuɗi
Shugabannin al’umma sun ce rashin kyawun hanyoyi ya sauƙaƙa kai hare-hare a yankin.
Mohammed Mohammed, mai magana da yawun Lilo da ƙauyukan maƙwabta, ya ce harin ya faru ranar Litinin a kan hanyar Lilo zuwa Gulubba yayin da sojoji ke raka ‘yan kasuwa zuwa kasuwar Gusau.
‘Yan bindiga da suka ɓoye a gefen hanya ne suka fito suka fara harbi.
Shaidu sun ce yawancin ‘yan kasuwar sun gudu cikin daji, domin tsira da rayukansu.
Maharan sun kashe sojoji biyar da ‘yan kasuwa kusan 10.
Al’ummar sun roƙi gwamnati a matakan ƙananan hukumomin, jiha da tarayya su tallafa musu wajen tsaro, ilimi, lafiya, da samar da hanyoyi.
Kakakin sojojin, Kyaftin David Adewusi, ya ce bai san da labarin harin ba amma zai yi bayani daga baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp