Wasu ‘yan bindiga a safiyar ranar Juma’a sun kashe ‘yan sanda biyar a mahadar Okpala da ke karamar hukumar Ngor Okpala a Jihar Imo.
Haka kuma an kashe wasu ma’aurata masu suna Mista da Misis Chinaka Nwagu wadanda suka fito daga yankin Amankwo Okpala.
- Sallah: Wamako Ya ‘Yantar Da Fursunoni 62 A Sakkwato
- Bukatar Magidanta Su Sa Ido Kan Yadda ‘Ya’yansu Za Su Yi Bikin Sallah
Lamarin dai ya jefa daukacin al’ummar yankin cikin firgici saboda ba zato ba tsammani aka kawo karshen harkokin kasuwanci.
Wani dan uwa ga ma’auratan ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan sandan da aka kashe sun taso ne daga sashin ‘yan sanda da ke makwabtaka da Abo Mbaise don cin abinci a mahadar.
Ya ce a yayin da ‘yan sandan ke cin abinci, wasu ‘yan bindiga sun zo wajen inda suka bude musu wuta.
Ya ce yayin da aka harbe ‘yan sanda uku a wurin, wasu biyu kuma sun gudu zuwa wani waje, amma maharan sun garzaya zuwa shagon da suka fake suka kashe su sannan suka kashe ma’auratan da ke shagon da suka shiga.
Wani ganau ya bayyana cewa bayan kashe ‘yan sandan, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da bindigunsu guda biyar.
Majiyar ta ce, “Wannan bakar rana ce a cikin al’ummarmu. Wasu ‘yan bindiga da misalin karfe 8 na safe sun harbe ‘yan sanda biyar har lahira a mahadar Okpala. ‘Yan sandan sun tuka motar Hilux mai launin fari daga sashin ‘yan sanda na Aboh Mbaise don cin abinci a mahadar.
“A lokacin da suke cin abinci, ‘yan bindigar sun dira wajen, suka bude musu wuta. Biyu daga cikin ‘yan sandan biyar sun garzaya zuwa wani shago don fakewa, amma suka bi su suka kashe su tare da wasu ma’aurata.
“Sun kwashe bindigoginsu. Wannan abin takaici ne sosai. Kowa ya rude. Ma’auratan sun yu kaura daga Legas kusan shekara daya da ta wuce. Mun ajiye gawarwakinsu a dakin ajiyar gawa. An rufe kasuwar. Mutane sun gudu sun bar shagunansu.
Wani mai suna Dominic Okpor ya shaida wa wakilinmu cewa ya ga gawarwakin ‘yan sandan da aka kashe a kan hanyar da ya bi ta hanyar Owerri zuwa Aba.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Henry Okoye, ya ce har yanzu ba shi da masaniya kan lamarin.