Wasu ‘Yan bindiga hudu dauke da muggan makamai a kan Mashina biyu sun bude wuta kan magoya bayan jam’iyyar APC a lokacin gangamin yakin neman zaben Sanatan Ebonyi ta tsakiya a kauyen Onuwankwo da ke gundumar Ezzagu ta 1, a karamar hukumar Ishielu da ke jihar Ebonyi tare da kashe wani mutum mai suna Mr. Emeka Nwusulor, tare da jikkata wasu mutum hudu.
LEADERSHIP ta rawaito cewa maharan sun kuma yi wa wurin wani gangamin yakin zaben APC kawanya a gundumar Agba da ke karamar hukumar Ishielu, inda a nan suka yi ta harbin iska. Sai dai ba a samu wani da ya jikkata a Agba ba.
- Dakatar Da Binani: Mazaba Ba Ta Da Ikon Dakatar Da Mutum Daga Jam’iyya -Sakataren APC
- PDP Ta Dakatar Da Shugabanta A Ebonyi Kan Yi Mata Zagon KasaÂ
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, shugaban karamar hukumar Ishielu, Mista Obinna Onwe, ya ce, lamarin ya faru ne wajajen karfe 5:30pm jim kadan bayan da aka kammala yakin neman zaben.
Ya misalta harin a matsayin abun tir da kaico, ya kara da cewa masu kai harin sun kuma kona wata mota kirar Hayis mallakar mijin Ko’odinetan kungiyar ci gaban Inyaba, Hon. Blessing Nweze, da kuma wata mota mallakin magoya bayan jam’iyyar.
Hon. Onwe ya ci gaba da cewa gawar wanda aka kashe an dauke ta zuwa dakin adana gawarwaki, yayin da kuma wadanda suka jikkata suke amsar kulawar Likitoci a wani asibitin da ba a bayyana sunansa ba.