‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu sabbin ma’aurata bayan kashe jami’an sa-kai biyu a wani hari da suka kai unguwar Shola da ke birnin Katsina.
A cewar mazauna unguwar, ‘yan bindigar sun far mu su ne da misalin karfe 1:25 na dare, kuma sun shafe sa’a guda su na harbe-harbe.
- 2023: Dan Yayan Buhari, Fatuhu Muhammed Ya Fice Daga APC
- NDLEA Ta Cafke Tsohon Sojan Da Ke Wa ‘Yan Bindiga Safarar Miyagun Kwayoyi
Sun shaida cewa ‘yan sa-kan sun rasa rayukansu ne a kokarin hana garkuwa da ma’auranta, sannan an jikkata wasu daga cikinsu.
Rahotanni na cewa dole ta sanya masu aikin sa-kai janye jiki bayan sun fahimci cewa ‘yan bindigar sun fi karfinsu.
Wani mazaunin unguwar ta Shola da ke cikin Katsina ya shaida wa manema labarai cewa :yan bindigar sun shiga unguwar ne a kan babura jiya dauke da bindigogi suna harbe-harbe.
Mutumin ya ce ‘yan bindigar sun fasa wani gida ta baya suka shiga. Al’amarin dai yayi sanadin mutuwar mutum biyu sanann mutum biyu suka jikkata.
Ya kuma ce baya ga ma’auratan akwai mutane da dama da aka sace, sai dai bai san adadinsu ba.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa wannan ba shi ne karon farko da mahara ke aukawa unguwar Shola ba, ko a watan da ya gabata ma ‘yan bindiga sun shiga yankin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya ce jami’ansu sun dukufa don kubutar da amarya da angon da aka yi awon gaba da su.
Gambo ya ce sun kubutar da wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su a kauyen Tandama cikin karmar hukumar Danja, bayan wani samame da suka kai maboyar ‘yan bidiga.
Haka kuma, ya ce a yankin karamar hukumar Safana ma, sun yi nasarar kashe wani kasurgumin dan bindiga, Albdulkarim Faca-Faca da mutanansa bakwai a karshen mako, bayan barin wutar da wani jirgin yaki ya yi akan maboyarsu.