Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki rukunin wasu gidaje a Dutsen Reme a karamar hukumar Bakori ta Jihar Katsina tare da yin garkuwa da mutane hudu.
Lamarin dai a cewar mazauna yankin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na daren ranar Juma’a.
- Manufarmu Tsaftace Sana’ar Dirama A Fadin Kasar Nan -Umar Gobir
- Sassauta Matakan Kandagarkin Cutar COVID-19 A Amurka Ya Haifar Da Mumunan Tasiri
A cewar wani Ahmed Ridwan, mazaunin Dutsen Reme, maharan sun yi amfani da ruwan sama kuma suka aiwatar da aikinsu ba tare da wata matsala ba.
“Mutanen kauye da ke kusa da Maska ne suka sanar da mu ta wayar tarho cewa ‘yan bindiga da dama sun nufo unguwarmu kuma nan take muka sanar da ‘yan sanda da sojoji. Amma da suka isa, tuni ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mutane hudu,” in ji Ridwan.
Malam Lawal Hamisu Maska, wanda ba ya nan a lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmaki gidansu, ya ce an sace ma’aikacin babbar kotun Funtuwa mai suna Bishir Shitu Sallau tare da wani Safiyanu, dalibin Kwalejin Ilimi da ke Abuja.
Ya ce, “Ba na nan lokacin da ’yan bindigar suka shiga gidanmu; Tuni Bishir da Safiyanu suka boye matansu a bandaki, sai da ‘yan bindigar suka fasa kofar suka nemi matan amma ba su gansu ba. Don haka suka tafi da mazajensu.”
A dalilin faruwar lamarin, Hamisu Maska ya ce zai tashi daga gidansa da kuma unguwar domin neman mafaka.
“Ni likita ne kuma aikina ne ya kawo ni Funtuwa daga Maska. Wannan rashin tsaro da ba ba zai bari na yi aikina yadda ya kamata ba,” inji shi.
A wajen aikin ne suka yi awon gaba da wata Lauratu Jibril da diyarta, bayan da mijinta Malam Jibril ya tsira da kyar.
Wata kanwar wanda aka kashe, Safarau Sanusi, ta ce ‘yan bindigar sun shiga yankin da misalin karfe 9:45 na dare.
“Lauratu sabuwar amarya ce, ba ta wuce kwana 30 a gidan miji ba kafin a sace ta. Lokacin da mijin ya ga ba haza, sai ya yi sauri ya tsere,” in ji ta.
A cewar mazauna garin kwanaki bakwai da suka gabata ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane biyu a wani gida.
Hakazalika, a makon da ya gabata, an sace wani Tajuddeen, mai gyaran taya, da matar wani Tanimu Mohammed da ke Unguwar Maitandama.