‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Da Malaman Kwalejin Kimiyya Ta Jihar Kaduna

Daga Suleiman Ibrahim

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari akan makarantar Nuhu Bamali Polytechnic, Zariya da ke jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da dalibai da malamai a makarantar tare da harbe guda daya nan take.
A cewar rahotanni da yawa, ‘yan bindigar sun kai hari makarantar ne da ke kan hanyar Zariya zuwa Kaduna a daren Alhamis.

Abdallah Shehu, jami’in hulda da jama’a na makarantar ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin amma bai yi cikakken bayani ba.

Akalla mutum daya aka harbe yayin da wasu suka samu raunuka yayin da masu garkuwar suka yi ta harbe-harbe don tsoratar da Daliban da Malamansu dake zaune cikin makarantar.

Har yanzu ba a tabbatar da yawan daliban da aka sace ba, amma a cewar wata majiya, malaman da aka sace sun hada da Mista Habila Nasai daga Sashin Nazarin ilimin bai-daya da kuma Mista Adamu Shehu Shika daga Sashin kididdiga (Accounting).

Kwanan nan, an samun irin wadannan hare-haren akan makarantun cikin Kaduna, kamar sace dalibai a Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da Jami’ar Greenfield.

Exit mobile version