Rundunar ‘yansandan Jihar Filato ta tabbatar da yin garkuwa da Rabaran Bung Dong a unguwar Ganawuri da ke karamar hukumar Riyom a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, ne ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Litinin a garin Jos.
- Uba Ya Yi Wa ‘Yarsa Fyade A Osun, Amma Ya Roki Ta Yafe Masa
- An Ceto Mutane Fiye Da 650 Da Girgizar Kasa Da Ta Auku A Lardin Sichuan Na Kasar Sin
A cewar Alabo, an sace Faston ne a ranar Lahadi da daddare, tare da wani Mista James Mann, wanda daga baya aka ceto shi.
Mann shi ne shugaban makarantar sakandiren gwamnati da ke Ganawuri kuma kanin babban alkalin jihar, mai shari’a David Mann.
Sai dai Alabo, ya ce rundunar ‘yan sandan ta baza jami’an tsaro a yankin domin zakulo masu laifin tare da kubutar da wanda aka sace.
A halin da ake ciki, Mista Song Moro, shugaban kungiyar Atten Youths Movement, ya ce al’umma sun dade suna fuskantar kalubalen tsaro sosai a yankin.
A cewarsa, an sace mutane akalla hudu a yankin kwanan nan.
Ya tabbatar da cewa ’yan kungiyar da ’yan banga a cikin al’umma ne suka ceto Mann daga hannun wadanda suka sace shi.
Moro ya ce masu garkuwa da mutanen suna neman a biya su kudin fansa Naira miliyan 20 domin a sako Fasto din.