‘Yan bindiga sun kai hari wani Masallaci da ke Gusau a Jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da gomman mutane yayin da ake tsaka da sallar Tahajjud.Â
A cewar wani mazaunin yankin da lamarin ya faru, ya ce maharan sun kutsa kai cikin masallacin tare da sace mutanen da ba a san adadinsu ba.
- Judith Suminwa Tuluka Ta Zama Mace Ta Farko Da Ta Zama Firaminista A Afrika
- Goman Ƙarshe Na Watan Ramadan [Darajarsu Da Mutsayinsu]
Mazaunin ya kara da cewa “Ba a san adadin mutanen da suka sace ba, amma hukumomi na ci gaba da bin sahun maharan.”
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, maharan ba su kira kowa domin neman kudin fansa ba.
Wannan harin na zuwa ne bayan da Gwamnan jihar, Dauda Lawal ke ci gaba da neman hadin kan hukumomin tsaro a Nijeriya don magance matsalar tsaro a jihar.
Idan za a tuna a makon da ya gabata ne, Gwamna Dauda Lawal ya tattauna da shugaba Bola Tinubu don nemo hanyar magance matsalolin tsaro da suka addabi jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp