‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 16 a ƙauyen Mararraba Mazuga da ke ƙaramar hukumar Kachia a Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru tsakanin ƙarfe 11 na daren ranar Alhamis zuwa ƙarfe 12 na safiyar Juma’a.
- Gwamna Sule Ya Rushe Majalisar Zartarwar Nasarawa, Ya Sauke Sakataren Gwamnati
- Tabbas Sin Za Ta Ci Gaba Da Jan Zarenta A 2025
Mutum biyu sun tsere daga hannun maharan, yayin da aka saki mutum bakwai don su nemo kuɗin fansar sauran mutanen da suka kama.
Daga cikin waɗanda ke tsare akwai ‘ya’ya biyu na wata mata mai suna Na’omi Kayit, sai mutum ɗaya daga cikin waɗanda aka saki.
Ɗaya daga cikin ‘ya’yan naga ɗaliba ce a ABU Zariya, yayin da ɗayar ke karatu a Togo.
Har yanzu, masu garkuwa da mutanen ba su tuntuɓi iyalan waɗanda suka kama don neman kuɗin fansa ba.
Ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna bai yi nasara ba, domin ba a samu kakakin rundunar ba, ASP Munsir Hassan.