An yi wa mutane uku yankan rago yayin da aka yi garkuwa da wasu da ba a tantance adadinsu ba a daren Laraba a unguwar Maguzawa da ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja.
Rahotanni da dama daga yankin sun ce daga cikin wadanda aka sace akwai mata da kananan yara yayin da mazauna yankin da dama suka tsere daga gidajensu zuwa Kagara da Pandogari a jihar Neja da kuma garin Birnin Gwari a jihar Kaduna.
- ‘Yan bindiga Sun Kai Hari Kauyuka 8 Da Kashe 33 Da Sace Mutum 30 Da Shanu 2,000 A Kebbi Da Neja,
- ‘Yan Boko Haram 204 Sun Mika Wuya Ga Sojoji A Jihar Borno
Maguzawa dai yana da tazarar kilomita 25 daga garin Kagara a jihar Neja da kuma kilomita 12 daga Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Hare-haren na Maguzawa ya zo ne kasa da sa’o’i 48 a lokacin da ‘yan bindiga suka kai wani hari a kauyen Gidigore da ke karamar hukumar Rafi, a daren ranar Talata, inda aka kashe akalla rayuka biyar tare da sace wasu da dama.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, “A Maguzawa, an kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu da ba a tantance adadinsu ba, wasu kuma sun gudu. Ya zuwa yanzu mun ga gawarwaki uku da aka yanka su. Ba mu san adadin mutanen da suka tafi tare da su ba a yanzu. ”
Mazauna yankin sun shaida cewa, makwanni uku da suka gabata an yi garkuwa da wasu a karamar hukumar Rafi da da yi musu fashi.
Wani mazaunin garin Ibrahim Ahmad ya ce dan uwansa na daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a daren ranar Talata, inda ya ce mutane da dama sun tsere daga gidajensu zuwa Kagara da Pandogari a jihar Neja da kuma kona Gwari a jihar Kaduna.
“A cikin kasa da makonni uku, mun ga hare-hare daban-daban har guda 10 a kan mutane daban-daban a karamar hukumar Rafi, kusan kowace rana.
Kafin harin na ranar Talata, makonni biyu da suka gabata, ‘yan bindiga sun kai hari a kauyukan Gulbi, Unguwan-Jaye da Kusherki inda aka kashe mutane 8 tare da yin garkuwa da wasu 36 yayin da mutum daya da ya samu munanan raunuka. A yayin da nake magana da ku, sun bukaci Naira miliyan 50 ga mutanen farko da suka yi garkuwa da su,” inji shi.
Ahmad ya ce an kona gidaje da kadarori na manoma da dama a harin na ranar Talata wanda ya dauki sa’o’i da dama.
Ya bukaci tallafin jin kai daga gwamnati, kungiyoyi da daidaikun jama’a musamman kayan abinci da yara kan sanyawa don rage musu kuncin rayuwa.
Al’umar Gidigore da aka kai harin na baya-bayan nan na da tazarar kilomita kadan daga garin Birnin Gwari na jihar Kaduna, inda ‘yan bindigar suka kai hare-hare da dama.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar harin na Didigore amma har yanzu bai tabbatar da sabon harin ba.
Ya ce, “A yayin harin, kimanin mutane uku ne suka rasa rayukansu, sannan an sace wasu da ba a tantance adadinsu ba, yayin da aka kona gidaje biyu.”